Ticker

6/recent/ticker-posts

Inna Leliya

6.59 Inna Leliya 

Wannan ma wasan gaɗa ne da ke buƙatar wasu adadin masu wasa da dama domin gudanar da shi. Kimanin yara ishirin zuwa sama da haka na haɗuwa domin gudanar da shi.

6.59.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Inna Leliya wasan gaɗa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare lokacin da akwai farin wata.

6.59.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira mai ɗan faɗi ta hanyar barin ‘yar tazara tsakanin juna. Daga nan ɗaya daga cikinsu za ta shigo tsakiya. Za ta riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya tana waƙa yayin da su kuma ke amsawa. A cikin wasan, sun kasance tamkar ‘yanuwan wadda ke tsakiya masu dangantaka irin ta uwa ko uba ko kishiya ko uwar kishiya ko miji ko uwar miji da makamantansu. Saboda haka, za ta riƙa gwada irin gaisuwar da za ta yi wa kowa yayin da ta zo gare ta. Ko dai gaisuwa cikin darajantawa da girmamawa, ko kuma gatsine da kallon hadarin kaji. Haka za ta zaga su gaba ɗaya. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Inna leliya in kin dawo,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: In kin dawo,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ni haka zan miki.

Amshi: Inna leliya.

Bayarwa: Na ƙara yin haka,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga gyarana.

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga alakoro,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ke uwar mijina,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: In kin dawo,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ni haka zan miki,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Naƙ ƙara yin haka,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga gyarana,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga alakoro,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ke Goggona,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: In kin dawo,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ni haka zan miki,

Amshi: Inna leliya.

Bayarwa: Naƙ ƙara yin haka,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga gyarana,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga alakoro,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ke kishiyata,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ke ‘yar banza,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ke ‘yar wofi,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: In kin dawo,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ni haka zan miki,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Nas sake yin haka,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga gyarana,

Amshi: Inna leliya.

 

Bayarwa: Ga alakoro,

Amshi: Inna leliya.

Kishiya ita ke zuwa ƙarshe. Sai mai waƙa ta gama ƙirgo sauran dangi kamar su baba da sarkuwa da inna da makamantansu, kafin kishiya ta zo ƙarshe.

6.59.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki da samar da nishaɗi ga yara. Sannan ta kasance tamkar madubi ko hoto da za a iya hango wani ɓangare na tsarin zamantakewar Bahaushe. Musamman abin da ya shafi girmama na gaba da kuma kishin da ke tsakanin kishiyoyi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments