Ticker

6/recent/ticker-posts

Carmama

6.57 Carmama 

Wannan ma wasa ne na yara mata. Yana cikin rukunin wasannin mata na dandali da ke tafiya da waƙa. Kamar mafi yawan wasannin dandali, shi ma da dare ake gudanar da shi, lokacin farin wata. Ba ya buƙatar kayan aiki yayin gudanarwa.

6.57.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya bisa tsarin da’ira. Daga nan sai ɗaya daga ciki ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa saura kuma na amsawa tare da tafi. Waƙar kuwa ita ce:

Bayarwa: Iye nanaye,

Ayye yaraye nanaye,

Carmama.

Amshi: Iye nanaye,

Ayye yaraye nanaye,

Carmama.

 

Bayarwa: Jirgin goro lula-lula,

Jirgin goro za ya kaɗe ni,

Jirgin goro kar ka kaɗe ni,

Jirgin goro zan maka saƙo,

Ba saƙon sayen tasa ba,

Ba saƙon sayen kwano ba,

In ka je ka gai da masoyi,

In ka je ka sa masa riga,

In ka je ka sa masa wando,

In ka je ka sa masa hula,

Ka sanya masa takalmin girma,

Carmama.

Amshi: Iye nanaye,

Ayye yaraye nanaye,

Carmama.

6.57.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Waƙar wasan tana ɗauke da saƙon soyayya. Sannan tana ɗauke da jigon ban dariya. Shin masoyin tsirara yake kafin jirgin goro ya je?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments