Ticker

6/recent/ticker-posts

Basha

6.4 Basha

Wasan Basha ma an fi yin sa a lokacin azumi. Sai dai shi ba tashe ba ne. Akan gudanar da wannan wasa a watan azumi musamman idan azumi ya kai ashirin.

6.4.1 Masu Wasa

‘Yan mata ke gudanar da wannan wasa, ‘yan kimanin shekaru goma sha huɗu (14) zuwa sama. Adadin masu gudanar da wasan yana da yawa. Domin a wasu lokuta, ‘yanunguwanni daban-daban ne sukan haɗu a wuri ɗaya domin yin wannan wasa.

6.4.2 Lokacin Da Wurin Wasa

i. Ana fara gudanar da wannan wasa ne tun rana (yayin da ‘yanmatan za su yi dafe-dafe da soye-soye) har zuwa dare. Wato dai bayan an yi buɗa-baki kuma an yi salloli, yayin da nan ne za a gudanar da asalin wasan.

ii. Ana gudanar da wannan wasa ne a dandali.

6.4.3 Kayan Aiki

i. Kayan girke-girke, kamar shinkafa da gishiri da mai da makamantansu.

ii. Zungurun ƙunshin lalle

6.4.4 Yadda Ake Aiwatar Da Wasan Basha

Ibrahim (Mrs) (2000: 13) ta kawo bayanin yadda ake wasan Basha a garin Gumel. ‘Yanmata na dafe-dafe da soye-soyen abinci iri-iri. Yawanci sukan samu kuɗin waɗannan girke-girke ne daga samarinsu ko kuma iyaye. Bayan an kammala, ‘yan matan za su take cikinsu tare da ƙannensu. Daga nan kuma sai kowace ta ɗauko zungurunta na ɗaure lalle ta hau yin lalle. Bayan lallen ya kama, sai kuma su ɗunguma zuwa dandalin unguwarsu.

A dandalin ne kuma za su haɗu da ‘yan matan sauran unguwanni daban-daban. Wani lokaci akan je gidajen ‘yan matan da ba su samu dammar fitowa wannan wasa ba domin a fiddo da su ko da ta tsiya-tsiya ne. ‘yan matan kan yi da’ira. Daga nan kuma za a zaɓi mata bibbiyu daga kowace unguwa (waɗanda su ne za su wakilci wannan unguwa). Waɗanda aka zaɓa za su koma tsakiyar da’ira. Daga nan kuma, za su riƙa bangazar juna da kafaɗa da ƙarfi. Za su yi hakan har sau goma. Amma yara cikinsu, waɗanda ƙarfinsu bai kai ba, sukan yi sau biyu ne kawai ko makamancin haka. Duk wadda ta yarda ta je ƙasa (faɗi), za a riƙa yi mata gori da cewa ita raguwa ce.

6.4.5 Waƙar Wasa

Iye ragargajenmu na faɗa mun zo.

Iye mun ƙi jinin faɗa mun ƙi rainin wayo,

Iye in mun so faɗa har mari mukan nema.

Iye ku kuma ƙarfi da ƙarfi.

Mene ne ƙarfin budurwa?

Basha ce ƙarfin budurwa.

Iye wadda ba ta da ƙarfi ta doka a sannu.

Iye doka a sannu don ba ki lalace ba.

Iye lalaci a nonon uwa akan tsotsa.

Iye ban tsotsa ba ko da a nonon Inna.

Iye a nonon Inna zinariya da azurfa.

Iye kowace shekara da shi muka ci muka sha.

Iye kowace shekara da shi muke daka gumba.

Iye mukan daka gumba har ma da yankar kaji.

Iye kajin ma farare muke yankawa.

6.4.6 Tsokaci

Wannan wasa yana koyar da jarumta. Sannan yana sanya haɗin kai tsakanin ‘yan mata, kamar yadda suke haɗuwa daga unguwanni daban-daban domin gudanar da wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments