Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Dela Ba Kande

6.48 Ba Dela Ba Kande

Wannan wasan mata ne da aka fi gudanarwa a dandali. Kamar mafi yawan wasannin dandali, akan yi shi ne da dare, lokacin farin wata. Yana cikin rukinin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa. Sai dai ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin mutane takwas zuwa sama ne suke gudanar da wasan.

6.48.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan  tsaya a tsarin da’ira. Daga nan sai ɗayarsu ta fito tsakiya, ta riƙa ba da waƙa. Sauran kuwa za su riƙa amsawa tare da tafi. Waƙar ita ce:

Bayarwa: Abokiyata,

Amshi: Iye.

 

Bayarwa: Tashi mu je itace,

Amshi: Iye nanaye.

 

Bayarwa: Ni ba ni zuwa itace,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Igiya ta ɓace mani,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Gammo ya ɓace mani,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Hanya ta ɓace mani,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Na yo kalmasa ta,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Karsa ya tare ni,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Ni ba ni magana da Karsa,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Karsa kuikuyo ne,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Sauna mai lakkar idanu,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Masoyi ruwan zuma ne,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Maƙiyi ruwan maɗaci,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Sannu masoyi sannu,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Hanya zan bi gobe,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Za ni gai da masoyi,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Taka rawar masoyi,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

A wannan gaɓa yara za su tiƙi rawa su more. Daga nan kuma wadda ke tsakiya za ta koma cikin sauran yara. Wata daban kuma za ta komo tsakiya domin a ci gaba da wasa.

6.48.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Waƙar wasan tana nuni ga ɗarsashin zuciyar ‘yan matan game da sosayya. Wannan tamkar wani saƙo ne ga iyayensu da kuma sauran masu sauraro. Bayan haka, Sannan tana isar da wani saƙo game da halayyar kare na wasu samari, wato bibiyar ‘yan mata. An yi amfani da salon kamantawa domin fito da wannan saƙo. Wato inda aka kamanta halayyar bibiyar mata da halin kuikuyo.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments