Ticker

6/recent/ticker-posts

Cin Dawo

6.47 Cin Dawo 

Wannan ma wasan yara mata ne. Yana rukunin wasannin zaune. Sannan yana tafiya da waƙa. Kimanin yara biyar zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasan ba ya buƙatar wasu kayan aiki na musamman.

6.47.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a cikin gida ko a dandali.

ii. Ana gudanar da wasan da hantsi ko da yamma (musamman a cikin gida) ko kuma da dare (musamman a dandali).

6.47.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Sai kuma su zauna su miƙe ƙafafunsu zuwa gaba. Sannan za su fara rera waƙa a tare. Sannan za su riƙa tafi tare da buga cinyoyinsu. Waƙar da ake rerawa a wannan wasa tana tafiya kamar haka:

Cin dawo cin dawo,

Ɗan fafarin fafara,

Uwar Ladi tana daka,

Na muƙa mata muciya,

Ta ce mene ne haka?

Na ce morewa na yi.

Ana yayin walƙiya,

Ana murza ƙuli-ƙuli,

Da me za mu ci zogala?

Da dinki da kwaɗon rama,

Da shi za mu ci zogala.

Tsohuwa za ta mutu,

Ba ta ce Allah ba,

Ba ta ce Annabi ba,

Sai ta ce:

Jada yalo,

Yana maganin mutuwa,

Sai ta sha sai ta mutu.

Sai ta je kasuwa,

Sai ta faɗa ma gyaɗa,

Ke gyaɗa bari magana,

Kuɗinki na aljihu,

Na auduga ba su zo ba.

6.47.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi da kuma annashuwa ga yara. Waƙar wasan ta waiwaici wasu abincin Hausawa da suka shafi kwaɗo. Sannan waƙar wasan na ɗauke da ban dariya. Domin morewa kawai sai a muƙa wa uwar Ladi muciya? Wataƙila tsohuwa ta mutu da kwaɗayin gyaɗa shi ya sa ta taso don neman ta a kasuwa bayan ta mutu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments