Ticker

6/recent/ticker-posts

Odada

6.49 Odada

Wannan ma wasan yara mata ne. Yara biyu zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yana da siga irin na babunna da kuma ɗayan.

6.49.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko gidajen bikin aure ko na haihuwa ko kuma wurin da yara mata ke taruwa.

6.49.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su tsaya a layi ɗaya. Wadda yin ta ne za ta fito gaban layi ta fuskance su. Daga nan za su kaɗa da ta farko a layi. Za su yi kaɗin ta hanyar waƙa da tafi da ‘yan tsalle-tsalle. Yayin da suka kai ƙarshen waƙar, za su yi ƙoƙarin buɗewa ko tsukewa. Idan suka bude ko suka tsuke sau uku tare, to an ƙwace mai yi. Idan kuwa sun saɓa, to mai yi za ta ci gaba zuwa mai wasa ta gaba.

6.49.3 WaƙarWasa

Odada odada,

Wan ‘yar alawa,

Tu ‘yar abun bana,

Ribisho ribishon,

Akwala ribishon,

Wan na ribishon,

Wanda ya nace amsa masa wan.

6.49.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana buƙatar lissafi da kuma zurfafa tunani. Abin zai burge mai kallo yayin da ya ga yara suna ƙoƙarin karantar tunanin juna yayin da ake wannan wasa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments