Ticker

6/recent/ticker-posts

Dinga-Dinga

6.46 Dinga-Dinga

Wannan ma wasa ne daga cikin wasannin tashe na mata. Kimanin mutane biyar zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Kamar sauran wasannin tashen mata, an fi gudanarwa da dare, bayan an sha ruwa; wato cikin watan azumi. Sannan akan bi gida-gida ne domin gudanar da tashen.

6.46.1 Kayan Aiki

Kayan mata tsoffi kuma marasa kyau. Misali:

i. Takalma

ii. Zane

iii. Riga

iv. Mayafi

v. Kallabi

6.46.2 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin yara za ta yi shiga mara kyau ta hanyar sanya kayayyakin da aka lissafo a ƙarƙashin 6.46.1. Za ta shige gaba sauran yara kuma na biye da ita. Yayin da suke cikin gida domin tashe, wannan yarinya za ta riƙa taku ɗaiɗai. A cikin sauran yara kuwa, ɗaya za ta riƙa ba da waƙa yayin da saura ke amsawa. Ga waƙar kamar haka:

Bayarwa: Dinga-dingar gaye,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Uwarta ba ta son ta,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ubanta ba ya son ta,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Saboda kayan salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ba ta da kayan salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ba ta da rigar salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ba ta da zanen salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ba ta takalmin salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: A ba ta ko ɗan sisi,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Ta samu kayan salla,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

 

Bayarwa: Dinga-dingar gaye,

Amshi: Shegiyar ‘yar banza!

Haka za su ci gaba da wannan waƙa yayin da Dinga kuwa ke ta faman zazzagawa da tsummokaran kaya jikinta. Wato dai ga salla ta zo amma saboda iyayenta sun ƙi ta, ba ta da kayan salla.

6.46.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga masu yi da kuma musamman masu kallo. Haƙiƙa bara ne cikin wayo. Dole ne a ji tausayin kasancewar Dinga ba ta da kayan salla, ga kuwa salla ta zo. Don haka sisin da aka roƙa a ba wa Dinga saboda ta samu kayan salla ba zai gagara ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments