Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Kwado

6.45 ‘Yar Ƙwado 

Wannan wasan yara mata ne da aka fi gudanarwa lokacin damina. Wato lokacin da ƙasa take da damshi. Tsarinsa ya yi kama da na wasan‘Yar Cafel. Sai dai sun bambanta ta wasu ɓangarori. Yara biyu ma sukan iya gudanar da wannan wasa a tsakaninsu. Amma yawansu na iya kasancewa sama da haka sosai.

6.45.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a gida ko wurin sauran yara ko makarantun boko.

ii. Ana wannan wasa da hantsi ko da yamma.

iii. Ƙwado

6.45.2 Kayan Aiki

i. Ƙananan duwatsu (tsakuwowi)

ii. Kara ko itace ko cokali ko wani abu makamancin wannan (domin tonon rami)

6.45.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi amfani da ɗaya daga cikin abubuwan da aka ambata a ƙarƙashin ‘ii’ na 6.45.2 domin su tona ƙaramin rami marar zurfi. Wato ɗan gurbi amma mai matsakaicin faɗi. Yawanci tsawonsa bai kai ramin wasan Carafke ba. Sai dai ya fi shi faɗi. Sannan kowacce za ta ɗebo duwatsu adadin da aka ƙayyade a hannunta.

Mai gudanar da wasa za ta zuba duwatsunta cikin wannan gurbi. Waɗannan duwatsu akan kira su da ‘ya’ya. Daga nan za ta riƙa jefa ƙwadonta sama tare da ɗaukar ‘ya ɗaya daga cikin ramin kafin ƙwado ya sauko ta cafe. Yayin da ta kasa café ƙwadon ko kuma ta gaza ɗauko ɗa daga cikin ramin, ko ta ɗauko sama da ɗaya, to ta faɗi. Don haka ta gefenta za ta karɓi wasa.

Haka za a ci gaba da wannan wasa. Duk wadda ta tsince duwatsunta kaf, to ta fita. Don haka za ta riƙa farin ciki tare da jiran abokan wasanta.

6.45.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga masu gudanarwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA 

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments