Ticker

6/recent/ticker-posts

Ni Kura-Kura

6.44 Ni Kura-Kura 

Wannan wasa ne da ke buƙatar a ƙalla mutane bakwai zuwa sama domin gudanar da shi. Daga cikinsu akwai kura wadda ita ce ke kamu. Sannan akwai uwa wadda ke ƙoƙarin kare ‘ya’yanta daga kura. Sai kuma ‘ya’ya waɗanda kura ke ƙaƙarin kamawa.

6.44.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Wannan wasa ne na dandali. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare. Sai dai yara na gudanar da shi a makarantun boko, musamman yanzu da aka samu yawaitar irin waɗannan makarantu.

6.44.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan kasance a kan layi ɗaya. Wato sukan jeru ɗaya a bayan ɗaya. Daga nan kowacce za ta kama kunkumin wadda ke gabanta da hannuwa biyu. Ta gaba a a wannan layi ita ke mazaunin uwa. Sauran da ke bayanta kuwa, duka ‘ya’yanta ne.

Ɗaya daga cikin yaran kuwa za ta kasance ba a cikin layin ba. Za ta zamanto a gaba, tana fuskantar su. Wato dai sun yi gaba da gaba da uwa. Wannan ita ake kira kura. Daga nan kura za ta riƙa waƙa uwa kuwa da ‘ya’yanta suna ba ta amsa kamar haka:

Kura: Ni kura kura,

Amshi: Ba kya ci ba!

 

Kura: Ni kurar sarki,

Amshi: Ba kya ci ba!

 

Kura: Ni ta galadima,

Amshi: Ba kya ci ba!

Kura: Wuuu sai na ci!

Amshi: Ba kya ci ba!

 

Kura: Wuuu sai na ci!

Amshi: Ba kya ci ba.

A duk lokacin da ta ambaci wuuu sai na ci¸za ta zabura ta nufi kan ‘yan wasan da nufin kama ɗaya daga cikinsu. Uwa kuwa za ta baza hannuwa da nufin tare kura daga kaiwa kan ‘ya’yanta. ‘Ya’yan kuwa za su riƙa ɓoyewa a bayan uwar. Duk wadda kura ta kama, to ta cinye ke nan. Wadda aka cinye kuwa ita ce za ta zama kura.

6.44.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments