Ticker

6/recent/ticker-posts

Kallo Da Ido

6.43 Kallo Da Ido

Wannan wasan tashe ne da yara mata ke yin sa. Yana da sigar wasan tashe na maza mai suna Jatau Mai Magani. Wasan sananne ne, don haka waƙar da ake gudanarwa ciki, da kuma shirin wasan ya bambanta daga wuri zuwa wuri. Sannan masu wasan sukan sauya wasu daga cikin kalaman waƙar, kasancewar tana da tsawo. Kimanin mutane bakwai zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

6.43.1 Kayan Aiki

Garin sabara ko lalle ko kuka ko dai gari makamancin wannan

i. Ledoji

ii. Kwanuka ko ƙore

iii. Layun wasa

6.43.2 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin ‘yanwasa za ta kasance mai maganin gargajiya. Wannan yarinya ita ce shugabar wasa. Za ta sanya layu a hannunta, ko dai ta ɗora su a cikin tarkacen kayan maganinta. Kayan maganin kuwa bai wuce garin sabara ko da lalle ko kuka, ko dai makamancin wannan. Wani lokaci akan ƙuƙƙulla wannan garin magani cikin ledoji, sannan a bar wani gari cikin ƙwarya ƙarama ko wani kwano.

Yayin da aka shiga gida domin tashe, jagora za ta baje kayan maganinta. Daga nan kuma za ta fara waƙa sauran kuma suna amsawa. Wani lokaci za ta riƙa ba wa abokan wasan nata garin magani a hannu, tamkar mai ba da maganin gaskiya. Waƙar kuwa ita ce:

Bayarwa: Kallo na ido,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Mata ga garin magani,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Mata ku fito ga magani,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Duk ku fito ga magani,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: A yau ni zan ba ku shi,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: In har ba ku san ni ba,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Ni ce mai magani,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: A nan kin ga na kishiya,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Idan kika karɓi na kishiya,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Baɗi ya war haka,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Kin kore kishiyoyi ɗari,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Nan kin ga na maigida,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Idan na ba ki na maigida,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Kullum ba ya ƙi ta taki ba,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Nan kin ga na arziki,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Domin ki kore tsiya.

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: A nan kin ga na haihuwa,

Amshi: Ɗangajere.

1,.

Bayarwa: Idan kin karɓi na haihuwa,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Ya war haka in mun je baɗi,

Amshi: Ɗangajere.

 

Bayarwa: Kin haife‘ya’ya ɗari.

Amshi: Ɗangajere.

Za ta riƙa wannan waƙa tana ƙoƙarin bayar da maganin, kamar dai da gaske abin da take faɗi duka gaskiya ne. Haka za su ci gaba da yi har sai an sallame su.

6.43.3 Tsokaci

Wannan wasa yana nuni ga wata al’adar Bahaushe, musamman kafin ya karɓi Addinin Musulunci. Wato al’adar karɓar magani domin samun biyan wata buƙata. Wannan ya haɗa da mallake miji da kuma korar kishiya.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments