Ticker

6/recent/ticker-posts

Kande Mahaukaciya

6.42 Kande Mahaukaciya 

Wannan ma wasan gaɗa ne. Misalin yara goma sha biyu ne suke gudanar da shi. Yawanci akan samu yarinya mai ƙaramin jiki sosai a matsayin ‘ya. Wannan ‘ya akan kira ta Kande Mahaukaciya a cikin wasan. Sannan akan sami wadda ta fi sauran girma a matsayin uwa.

6.42.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko gidan bukukuwa irin na suna da na haihuwa.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare.

6.42.2 Yadda Ake Wasa

Uwa za ta zauna ta ɗora ‘yarta a cinya. Daga nan kuma sauran ‘yan wasa za su zo su yi sallama tare da tambayar cewa za su sha ruwa, kamar haka:

‘Yan Wasa: “Assalamu alaikum za mu sha ruwa.”

Uwa: “Ku sha.”

Daga nan za su yi alamar sun ɗebo ruwa sun kawo zuwa hanci sannan sun shanshana. Sai kuma su ce:

‘Yan Wasa: “Iya iya moɗar taki da wari.”

Za ta yi shiru ba za ta kula su ba. Sai su juya kamar za su fita. Har sai sun yi nisa sai kuma su sake dawowa. Daga nan za su fara magana cikin waƙa yayin da uwar za ta riƙa ba su amsa cikin waƙa, kamar haka:

‘Yan Wasa: Assalamu alaikum Kande tana nan?

Uwa: Wace Kande?

‘Yan Wasa: Kande mahaukaciya.

Uwa: ‘Yar tawa?

‘Yan Wasa: Kande mahaukaciya.

Uwa: Ta cikina?

‘Yan Wasa: Kande mahaukaciya.

Uwa: Zan tashi!

‘Yan Wasa: Tashi baƙar kuliya!

Daga nan sai ta tashi ta bi su da gudu ta bar Kande nan zaune. Yara kuwa kowa zai watse su yi ta gudu. Duk wadda ta kama to ita ce za ta zama uwa a wasan gaba.

6.42.3 Tsokaci

Wannan wasa ne na nishaɗi tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jini gare su. Baya ga haka, wasan yana hannunka-mai-sanda game da abin da ya shafi tsafta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments