Ticker

6/recent/ticker-posts

Ragadada

6.41 Ragadada 

Wannan na ɗaya daga cikin wasannin mata na tashe da ya sanu sosai. Kimanin yara shida zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Sukan bi gida-gida bayan shan ruwa a watan Ramalara (watan azumi).

6.41.1 Kayan Aiki

Kayan sawa tsoffi marasa kyau

6.41.2 Yadda Ake Wasa

Akan yi wa ɗaya daga cikin masu wasa shigar tsoffin kaya, kuma marasa kyau. Za ta zama tamkar ƙazama da take cikin rashi (rashin kuɗi). Daga nan yara za su fara bi gida-gida. Duk gidan da suka isa, za su fara waƙa. Zabiya za ta riƙa ba da waƙar, saura kuma na amsawa.

A ɗaya ɓangaren kuma, wadda aka yi wa shigar kaya marasa kyau za ta riƙa taku ɗaiɗai. Wato dai ana nuna da ita ake magana a cikin waƙar. Waƙar kuwa ita ce:

Bayarwa: Ragadada

Amshi: Ta hana ki riga.

 

Bayarwa: Ragadada,

Amshi: Ta hana ki zane.

 

Bayarwa: Ragadada,

Amshi: Ta hana ki ɗankwali.

 

Bayarwa: Tsire,

Amshi: Ya hana ki riga.

 

Bayarwa: Tsire,

Amshi: Ya hana ki zane.

 

Bayarwa: Tsire,

Amshi: Ya hana ki ɗankwali.

 

Bayarwa: Balangu,

Amshi: Ya hana ki riga.

 

Bayarwa: Balangu,

Amshi: Ya hana ki zane.

 

Bayarwa: Balangu,

Amshi: Ya hana ki ɗankwali.

Haka za a yi ta lissafo abinci musamman dangin ƙwalama, ana kuma nuna cewa su ne suka hana ta yin arziki. Sannan kwaɗayinsu ne ya sanya mata tsiya, wadda har ba ta iya ɗinka kayan ƙwarai.

6.41.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallonsa. Sannan yana ɗauke da faɗakarwa game da kwaɗayi. Yana nuni da cewa, kwaɗayi na jefa ɗan Adam ga wahalar rayuwa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments