Ticker

6/recent/ticker-posts

Samodara

6.3 Samodara

Wannan ma wasan tashe ne wanda ake gudanarwa a watan azumi. ‘yanmata ne ke gudanar da wannan wasa, masu kimanin shekaru tara (9) zuwa sama. Ɗaya daga cikinsu za ta kasance Samodara, wadda kuma ita ce za ta riƙa ba da waƙa saura na amsawa. Kimanin yara biyar (5) zuwa sama ke gunadar da wannan wasa.

6.3.1 Lokacin Da Wurin Wasa

i. Akan gudanar da wasan Samodara ne a watan azumi, kasancewarsa wasan da ne. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko da dare. Ya dai danganta da lokacin da yara suka haɗu domin gudanar da wasan.

ii. Wannan wasa ba shi da wurin gudanarwa takamaimai. Domin kuwa, yara kan bi gida-gida ne suna aiwatar da shi, kamar dai yadda ake sauran tashen gida.

6.3.2 Kayan Aiki

i. Kayan shafe-shafe na mata, kamar su jambaki da gazal da hoda da makamantansu

ii. Kayan sawa na mata tsoffi ko marasa kyau.

6.3.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasan Samodara

Samodara (jagora) takan sanya tufafi marasa kyau. Sannan takan yi kwalliya da abubuwan shafe-shafe dangin jan-baki da hoda da ja-gira da gazal da makamantansu. Yawanci takan yi kwalliyar ba bisa tsari ba. Ma’ana takan laɓuna a wuraren da ba su dace ba, yadda da ka gane ta, za ka ga ba ta iya kwalliyar ba, ko kwalliyar ba ta yi kyau ba.

Daga nan yaran za su riƙa bi gida-gida inda Samodara za ta riƙa ba da waƙa saura na amsawa. Yayin da take waƙar, za ta riƙa nuna kayayyakin jikinta ɗaya bayan ɗaya tana cewa babanta ne ya saya mata, sannan ya ce ta yi yanga. Kuma za ta riƙa taku ɗaiɗai irin na yanga, ta re da fari da ido da kuma ɗangale hannaye, duk dai na nuna tana yanga.

6.3.4 WaƙarWasa

Samodara/Jagora: Iya duba-duba,

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Iya duba cikina.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Baba ne ya siya min.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Sai ya ce in yi yanga.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Ni ko yangar zan yi.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Iya duba sarƙata,

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Baba ne ya saya min.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Wai don in yi yanga.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: To ga yangar nan.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Iya duba zanena.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Baba ne ya saya min.

‘Y/Amshi: Samodara!

 

Samodara/Jagora: Kuma ya ce in yi yanga.

‘Y/Amshi: Samodara!

Samodara/Jagora: Ni ko yangar zan yi.

‘Y/Amshi: Samodara! 

6.3.5 Tsokaci

Wannan wasa yana nuni da mutum ya dogara da abin da Allah Ya ba shi, kuma ya yi alfahari da shi. Ga shi dai samodara ta kasance cikin kaya marasa daraja. Amma saboda wadatar zuci, sai ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali tamkar sarauniya. Baya ga haga, waƙar Samodara tana koyar da yaba wa kyauta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments