Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
6.3.3 Ilmantarwa/Karantarwa
Wani
Jigo da ake samu a cikin waƙoƙin bara shi ne ilmantarwa. Ilmantarwa a nan yana nufin karantarwa.
Jigon ilmantarwa shi ne wanda ke ƙunsar ilmin
yadda ake aiwatar da wata ibada a cikinsa. Irin wannan jigo a cikin waƙoƙin bara kamar
kumbo kamar kayanta ne. Wato babu wani bayani na ilmi sosai a cikinsa, da yake
masu tsara waƙoƙin su rera su ba masu cikakken ilmi ba ne. Da yawansu
Almajirai ne ko Gardawa ko sauran mabrata kamar makahi da masu wata naƙasa. Suna tsara waƙoƙin ne domin jawo hankalin masu ba su sadaka a maimakon su
je masu hannu rabbana, don haka ɗan ilmin da ake ambato a ciki bai taka kara ya karya ba. Manufar samun
wannan jigo a cikin waƙoƙin shi ne waɗanda ake yi wa bara musamman marasa ilmi daga ciki su ji kamar mai rera waƙar malami ne saboda girman da ilmi yake da shi. Misalin
wannan shi ne waƙar “Laƙada Raliyallahu” wadda a ciki ake cewa:
Jagora: Laƙada raliyallahu anal muminina.
Amshi: To.
Jagora: Angal lahu angaruhin
mu’asha.
Amshi: To.
Jagora: Inna in
sallah ki kai ki ɗauro da
niyya,
Amshi: To,
Jagora: In Azumi ki kai ki ɗauro da niyya,
Amshi: To,
Jagora: In zakka ki kai ki ɗauro da niyya,
Amshi: To,
Jagora: In tsalki ki kai ki ɗauro da niyya,
Amshi: To,
(Laƙad Raliyal Lahu)
A cikin wannan waƙar mai barar na ilmantar da wadda yake yi wa bara muhimmancin niyya ga kowane aiki na ibada. Sai dai kamar yadda aka faɗa can baya masu waƙar ba malamai ba ne, don haka ɗan abin da za su faɗa ƙalilan ne. A waƙar da ta gabata tun daga layi na uku har zuwa ƙarshe ana sanar da mai saurare matsayin niyya a cikin aiki. Kusan ana sanar da shi cewa niyya ita ce ƙashin bayan kowane aiki na ibada. Wannan shi ya sa aka ambaci shikashikan Musulunci daga cikin biyar kuma kowane aka jaddada yin niya wajen yin sa. Aka fara ambaton sallah tare da jawo hankalin wadda ake yi wa bara cewa ta fara ɗaura niya idan za ta yi. Haka sauran ibadu na azumi da zakka. Daga ƙarshe a ɗa na huɗu wanda shi ya kamata a fara ambata, wato tsarkin zuciya wanda shi ne imanin da ayyukan suka rataya gare shi. Babu shakka ɗiyan waƙar da suka gabata ko ba su yi bayani mai yawa ba sun sanar da mai sauraro cewa aiki ba ya inganta sai da niya.
Da yake
mabarata da yawa ba masu ilmi ba ne, ya sa waƙoƙinsu na ilmantarwa ba su da yawa. Ƙila shawar wannan jigo ya kai su ga aron rubutattun waƙoƙin ilmantarwa masu yawa suna bara da su. Kamar yadda aka
ambata baya, rubutattun waƙoƙi an nazarin jigoginsu a matakan bincike dabam-daban,
amma an kawo wani misali daga “Waƙar Kiran
Sallah” wadda take rubutatta ce kuma mabarata da yawa na amfani da ita wajen
yin bara domin misali kawai ba domin wani sabon nazari ba.
Allahu akbar in kiran sallah
kakai,
Don kak ka ce ala ka faɗi ga banza.
Wannan alifi ɗamre kablasan shikai
Ak, kak ka ce akabar a bar ka ga banza.
Akubar da akibar wanga dud
dulginku na,
Juhala’u kau da ka buɗe baki banza.
Kuma ba a cewa bar batun akbar
akai,
Don kakka tashi ka buɗe baki banza.
(Barmo Kwasare:Waƙar Kiran Sallah)
A waƙar marubucin yana ilmantar da jama’a ne a kan yadda ake
yin kiran sallah. Dubi yadda yake bayani a baiti na farko da na uku har ma da
sauran baitocin.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.