Ticker

6/recent/ticker-posts

6.3.2 Madahu/ Yabo

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

6.3.2 Madahu/ Yabo

Kalmar madahu an samo asalinta ne daga Larabci, wato “Madhu”, wadda take nufin yabo (Garba:1992).

“Madahu shi ne yabon Annabi Muhammadu tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi” Lawal (2004). Wannan jigon na madahu yana cikin jigogin da ke ƙunshe a cikin waƙoƙin bara da mabarata ke amfani da su. Akwai waƙoƙin bara da aka tsara domin begen Annabi kuma ake bara da su. Wasu daga cikin waƙoƙin bara masu ɗauke da jigon madahu na baka ne waɗanda aka shirya domin a yi bara da su. Irin waɗannan waƙoƙin da ma saboda bara aka yi su amma suka ƙunshe bege domin jawo hankalin masu saurare su ba mai rera su sadaka. Daga cikin irin waɗannan waƙoƙin akwai waƙar “Yabon Annabi” mai cewa:

 Jagora: To bisimilla Rabbi zan fara waƙa,

 Amshi: To.

 Jagora: In yi yabon Rasulu in samu lada.

 Amshi: To.

 Jagora : Kway yi yabon Rasulu ya gode Allah

 Amshi: To.

 Jagora: To daɗa zuciyarsa ta samu tsalki.

 Amshi: To.

(Yabon Annabi)

Waƙar da ta gabata waƙar bara ce ta begen Annabi (SAW). Idan aka lura tun wajen buɗa waƙar a ɗa na farko aka ambaci jigonta da cewa:

To bisimilla Rabbi zan fara waƙa,

In yi yabon Rasulu in samu lada.

Wannan ɗa ya fito da jigon waƙar ƙarara cewa waƙar ta madahu ce. Haka kuma an kawo wani tubalin gina jigon na madahu a cikin waƙar a inda ake ceawa:

 Annabi ya hito da haske da kyawo,

 Kowa ya gane shi ya ɗora murna,

 Ita ko ta gane shi ta ɗora kuka.

 Ke wannan barewa mi ad dalili,

 Kowa ya gane ni ya ɗora murna,

 Ke ko ke gane ni ke ɗora kuka.

 Ba kukan rashin ɗiya niy da shi ba,

 Don ƙamnar Rasulu Manzo fiyayye.

 (Yabon Annabi)

A lura da cewa tubalai biyu ne daga cikin tubalan gina jigon madahu aka ambata, wato haske da kuma mu’ujiza waɗanda na cikin tubalan da Yahya (1997) ya ambata a matsayn tubalan gina jigon madahu. A cikin waƙar an kira Annabi da haske aka kuma nuna wata mu’jiza tasa ta yin zance da barewa. Wato a taƙaice an yabi Annabi da kwatanta shi da haske da mu’jizar annabci da ya nuna na yin zance da barewa wadda take dabba ce da ba a san ta da yin magana ba. Haka ma a waƙar “Muhammadu Zaɓaɓɓe” ana cewa:

Allahu na yi roƙonka ka ban iko sarki,

Ka sa ni in yi begen Muhammadu zaɓaɓɓe.

Sarkinmu na da kyauta ba za ta iyaka ba,

Ya baka babu sarkin da zai amshe ma ba.

 (Muhammadu Zaɓaɓɓe)

A ɗiyan da suka gabata su ma sun nuna jigon waƙar madahu ne, domin shi mabaracin shi ne yake son yi kuma shi ne yake roƙon Allah ya ba shi ikon aiwatarwa. Haka ma aɗango na biyu ne ya kawo wani tubali na gina jigon yabo, wato kyauta. An nuna kyautar Annabi mai yawa ce har ba a iya cewa ga iya wajen da ta tsaya.

Su ma rubutattun waƙoƙin da mabarata ke bara da su akwai masu ƙunshe da jigon madahu. Irin waɗannan waƙoƙin suna da yawan gaske waɗanda malamai ke wallafawa saboda madahu amma kuma mabarata su mayar da su nasu su riƙa bara da su. Daga ciki akwai waƙar Imfiraji wadda ta yi fice kuma aka fi jin ta a bakin mabarata. Ga misali daga cikin waƙar:

 1. Bismillahil Majidi,

Nai nufin waƙa jadidi,

In yabon Ɗan nan Hamidi,

Zushafa yaumal mi’adi,

 Mai sonsa ba zai baƙin ciki ba.

 2. Rabbana yi daɗin aminci,

Gun Mafificin mutunci,

Ɗa wani nasa don karimci,

Wanda kab ba shuganci,

 Ya yi horo ba da kangara ba.

 3. Gaisuwata ko ta dace,

Gun Ma’aikin nan da an ce,

Ran Musulmi kar shi sance,

Bisa sonsa mu kau amince,

 Mai sonsa ba zai baƙin ciki ba.

 (Aliyu Namangi: Imfiraji)

Tun a wajen buɗa waƙar mawallafinta ya faɗi madahu zai yi a baiti na ɗaya layi na biyu da na uku wajen da ya ce:

Nai nufin waƙa jadidi,

In yabon Ɗan nan Hamidi,

Ya ambaci manufarsa na cewa zai yi sabuwar waƙa domin ɗan nan da ka sani da sifar hamidi wato Annabi Muhammadu (SAW) ke nan. Haka ma ya fara kawo tubalan gina madahu tun a wannan baitin na farko layi na huɗu wajen da ya ce:

Zu shafa yaumal mi’adi

Ma’ana mai ceto a ranar tashin Ƙiyama. Ya ci gaba da kawo wani tubali a baiti na biyu layi na biyu ya ce:

Gun Mafificin mutunci

Kalmar mafifici wani tubali ne na gina madahu, dukan kalmomin biyu wato ceto da fifiko tubalan gina madahu ne kamar yadda Yahya (1997) ya ambata.

Akwai rubutattun waƙoƙin madahu masu yawan gaske da malamai suka wallafa mabarata ke amfani da su wajen yin bara duk da su mawallafan ba domin bara suka wallafa su ba. Sake kawo waɗannan waƙoƙi a nan maimaita aiki ne domin an nazarce su a matsayin rubutattun waƙoƙin madahu a matakai dabam-daban. Wannan an kawo ta ne kawai domin misali.


Post a Comment

0 Comments