Ticker

6/recent/ticker-posts

Nishaɗantarwa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

6.3.4 Nishaɗantarwa

Nishaɗantarwa shi ne saka raha a cikin zuciya. Nishaɗantarwa a cikin waƙa na nufin saka nishaɗi da raha da annashuwa tare da bayar da dariya Gusau (2007). Nishaɗantarwa ke nan shi ne holewa, wato mutum ya sami ko ya kalli ko ya saurari abin da yake so a lokacin da yake hutawa. Nishaɗantarwa wani jigo ne da mabarata kan shigar a cikin waƙoƙinsu domin saka raha ga waɗan da suke yi wa bara domin su tasirantu su ba su sadaka ba a cikin damuwa ba. Ga misalin wasu daga ciki:

 Jagora: Suna suna na sani

 Amshi: To

 Jagora: Sunan dambu maƙura

 Amshi: To

 Jagora: In babu ruwa ɓanna yakai

 Amshi: To

 Jagora: Sunan kwaɗɗo Macciɗo

 Amshi: To

 Jagora: Su Macciɗo sai sanyin ɗuwai

 Amshi: To

 Jagora: Sunan zaure Babuga

 Amshi: To

 Jagora: Sunan tantabara Kulu

 Amshi: To

 Jagora: Sunan hankaka Ige

 Amshi: To

 Jagora: Sunan hanya Lailatu

 Amshi: To

 Jagora: Sunan luddai Ummaru

 Amshi: To

(Suna Suna)

 

A waƙar da ta gabata an ga yadda almajiri ya ba wasu abubuwa suna bayan wanda aka san su da shi ta hanyar dubin sifarsu da ɗabi’arsu domin ya ba masu sauraren sa dariya su sami nishaɗi. Ya kira dambu maƙura ta dubin halayya, ya kira mota gargaɗa ita ma saboda halayyarta, ya kira maciji Auwalu saboda dubin halittarsa, da dai sauran abubuwan da ya ambata ya ba suna. Duk ya yi wannan ne domi ba mutane dariya da saka masu nishaɗi ta yadda zai burge su ya samu sadaka. Haka ma a wata waƙar ake cewa:

 

Jagora: Su likkiɗa mini damu,

Amshi: To

Jagora: In karkace hulata,

Amshi: To

Jagora: In rangaɗa ma cikina,

Amshi: To

Jagora: Ciwon ciki ya yi sauƙi.

 (Waƙar Damu)

Waɗannan ɗiyan waƙar da suka gabata mabarata ke amfani da su a cikin waƙoƙinsu na baran domin su bayar da nishaɗi ga waɗan da suke yi wa bara. Dubi abin da suke faɗa mai bayar da dariya, kamar karkace hula idan za a sha fura saboda sanin daɗinta. Haka ma cewa in rangaɗa ma cikina a maimakon cewa in sha, duk kalmomi ne da aka yi amfani da su domin bayar da dariya ga mai sauraro. Ya nuna da zarar haka ta samu to ciwon cikinsa ya warke. Wannan kamar yana nuna babu wani ciwon ciki a tare da shi in ban da yunwa. 

Post a Comment

0 Comments