Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabana Gaba Nawa

6.33 Gabana Gaba Nawa

Wannan wasa ne na yara mata wadda yake kama da tafa-tafa. Sai dai wannan wasa a zaune ake yin sa. Sannan waƙar da ake yi yayin wasa hannuwa sun bambanta. Amma wuri da lokacin wasan daidai yake da na wasar tafa-tafa.

6.33.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan zauna su fuskanci juna. Sannan sukan naɗe ƙafafuwansu tamkar zaman karatun allo. Za su zauna ne kusa da juna. Daga nan za su fara waƙa tare da tafa hannu cikinsa lailai iri-iri. Za kuma su riƙa dafa ƙirjinsu yayin da suke wannan tafawa. Waƙar da suke yi kuwa ita ce:

Gabana gaba nawa,

Gabana kurciya gaba nafara,

In samu kurciya in harbe ta,

Tana baka-baka da ɗan baki,

Tana fiki-fiki da ɗan ƙoto,

Tana fuffuka da fuka-fuki.

6.33.2 Tsokaci

Waƙar wannan wasa na ɗauke da wasa da harshe. Hakan na samar wa yara gogewa wurin ƙwarewa game da amfani da harshe.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments