Ticker

6/recent/ticker-posts

Jallu Wa Jallu

6.32 Jallu Wa Jallu

Wannan wasa ne na dandali wanda mata a ƙalla goma suke gudanarwa. Wato dai yawan masu gudanarwa na farawa daga goma zuwa sama.

6.32.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare. Sai dai a zamanance da ake samun ‘yan makaranta na gudanar da wannan wasa yayin wasannin suna makaranta.

6.32.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi layuka biyu, su riƙa fuskantar juna. Wato kowace zai kasance akwai wadda take fuskanta. Amma za a bar tazara mai faɗi a tsakani. Kowane layi da aka yi akan kira shi da gari. Za a samu ɗaya ta taso daga cikin gari guda ta nufi ɗaya garin tana tafi tare da waƙa. Sauran masu wasa kuma za su riƙa amsawa. Waƙar takan kasance kamar haka:

Mai Bayarwa: Jallu wa jallu jallu wa jallu,

Amsawa: Jalluwal Larai.

Mai Bayarwa: Yaro ya riga ya saba,

Amsawa: Jalluwal Larai.

Mai Bayarwa: Alo-alo Sima taho,

Amsawa: Jalluwal Larai.

Da zarar an kawo wannan gaɓa ta waƙa, wadda take seti da mai waƙar za ta biyo ta. Za su riƙa tafiya cikin tsalle da tafi zuwa garin wadda ta taso da farko. Yayin da aka je kusa da garin wadda ta taso da farko, wadda ta taso da farkon za ta koma wurinta na asali. Na gefenta kuma za ta rako wannan ‘yar gari. Haka za su koma da waƙa da tafi da tsalle-tsalle. Yayin da suka je wancan garin, wadda ta fito da fari za ta koma wurinta, ta gefenta kuma za ta rako wannan.

Haka za a ci gaba da rakiyar kura, har sai kowacce ta yi rakiya. Da zarar kowa ta kamala rakiya, sai kuma a yi canjin gida. ‘Yan kowane gida za su taso cikin tsalle-tsalle da rawa da tafi tare da waƙar jallu wa jallu har sai sun koma gurbin garin juna. Daga nan sai a sake wasa daga fari. Haka za a yi ta yi har sai an gaji.

6.32.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan masu wasa na samun nishaɗi da annushuwa daga wannan wasa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments