Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
6.3.1 Wa’azi
“Wa’azi shi ne jawabi kan abin da ya kamata Musulmi ya yi da abin da bai kamata ya yi ba, ta kawo hujjoji daga Ƙur’ani da Sunna, da niyar mai da al’ummar Musulmi tafarkin gaskiya.”(CNHN:2006)
Haka kuma Hornby ya ce:
“Wa’azi shi ne yin jawabin da ya shafi addini.” Hornby (1998).
Ke nan jigogin wa’azi na nufin
ambaton wasu kalamai a cikin waƙa masu
dangantaka da addini da niyar shiryar da Musulmi ga tafarki madaidaici da kuma
tsoratar da su daga barin wannan tafarkin. Wannan jigo na wa’azi na ɗaya daga cikin jigogin waƙoƙin bara da
mabarata ke amfani da su a wajen bara. Wannan ya haɗa da waƙoƙin da su mabarata suka ƙirƙira domin yin bara da ma waɗanda aka rubuta ba domin bara ba amma suka kasance a kan
jigon wa’azi. Misali:
Kai azumi ka fidda zakka ka rage faɗa,
Ka rage bin san maƙwabci da itatuwa,
Ranar lahira
makwabcinka zumunka ne,
Ko nan duniya maƙwabcinka
zumunka ne,
Jirgi ɗan
Amina alkawarin duniya.
(Jirgi Ɗan Amina)
Waƙar da aka ciro wannan ɗa waƙa ce ta baka da mabarata ke rerawa sadda suke bara. A ciki suna horon Musulmai da su yi ayukan ɗa’a da Ubangiji ya yi umurnin a yi, kamar azumi da zakka. Haka kuma suna gargaɗin Musulmi da ya nisanci wasu miyagun halaye da Musulunci ya yi hani ga aikata su, kamar cutar da maƙoci.
A wani wurin kuma:
Jagora: Je ki marowaci ka sake
dubara.
Amshi: To.
Jagora: Ranar lahira kana ci da kuka.
Amshi: To.
Jagora: Kai kukan jini ka koma na
tilas.
Amshi: To.
Jagora: Ba ka da ɗan ƙane bare ɗan
aboki.
Amshi: To.
(Laƙada Raliyallahu)
Waɗɗanan ɗiyan waƙa ma wa’zi ne suke yi ga Musulmi na su nisanci yin rowa, domin yin rowa na haifar da haɗuwa da azabar ranar Lahira, ranar da babu wani mataimaki. Ambaton irin wannan kalami na iya tasiri ga zuciyar wanda ake yi wa bara ya bayar da sadaka.
Haka kuma a wata waƙar suna cewa:
Jagora: Wani na tuƙin mota ya bar ta ya tahi lahira.
Amshi: Baka.
Jagora: Wani na tuƙin jirgi ya bar shi ya tahi lahira.
Amshi: Baka.
Jagora: Wani na da gidan sama ya bar shi ya
tahi lahira.
Amshi: Baka.
Jagora: Wani na da gidan ƙasa ya bar shi ya tahi lahira.
Amshi: Baka.
Jagora: Baka bakariya baka da manyan kunnuwa.
Amshi: Baka.
(Waƙar Baka)
Su ma waɗɗanan ɗiya wani nau’in wa’azi ne mai nuna rashin tabbas ga rayuwar duniya. Ana kiran wannan nau’i na wa’azi da Zuhudu. A ɗiyan waƙar ana nuna yadda mutum ke mutuwa yabar abin da yake so, kuma ba makawa ga aukuwar haka a kan kowa. Su ma irin waɗannan kalamai na iya karya zuciya su sa waɗanda ake yi wa bara su bayar da sadaka.
Haka ma mabarata
sukan ɗauki rubutattun
waƙoƙin wa’azi su riƙa bara da su. Misali waƙar Gangara Wa’azu:
95. Wanda bai tsarin matarsa ba,
Kan yai ibada ladan ba yawa.
99. Wanda bai tsarin matansa ba,
Rantse ba zai ga Muhammadu Mahdi ba.
(Muhammadu Nabirnin Gwari: Gangar Wa’azu)
A baitocin da
suka gabata wa’azi ne ga Musulmi na su kula da kai da kawon iyalansu, wato ya
zama fitarsu ta kasance kan ƙa’ida ba
barkatai ba. Rashin yin haka na iya haifar da Allah ya ƙi karɓar
sauran ibadunsa da yake yi domin ya saɓa sunnar Annabi. Saɓawar
sunnar Annabi na iya zama dalilin rashin samun tsira Lahira.
75. “kar ka so bidia ta zamna,
Zuciyarka bale hiyana,
Kar ka zan mai son ka raina,
‘Yan’uwa ka tsare amana,
Ku bi sunna ba da kangara ba.
76. ‘Yan’uwa mu tsare iyali,
Sabulu da rini da lalle,
Duk mu sai masu in da hali,
In fita ko yai dalili,
To ka ram masu ba su je kawai ba”.
(Aliyu Namangi: Imfiraji ta uku)
Su ma waɗannan baitoci suna garagaɗi ga Musulmi ya guje wa wasu miyagun halaye kamar aikata bidi’a da cin amana da rena mutane . Haka akwai lurar da Musulmi game da tsare iyali tare da ɗaukar takalifinsu na yau da kullum da kuma saka ƙa’ida ga fitarsu.
Har ila yau akwai wannan jigon na
wa’azi a wata waƙar baran kamar
haka:
45. Ƙarya namima munafunci,
Mai yinsu ba za
shi tsira ba.
46. Da ci da ceto da ha’inci,
Mai yin su ba za
shi tsira ba.
47. Haka shan giya da girman kai,
Mai yin su ba za
shi tsira ba.
48. Mu daina ƙwace mu bar fahara,
Mai yin su ba za
shi tsira ba.
49. Da mai halatta haramiya,
Wallahi ba za shi
tsira ba.
(Zainu Bunguɗu: Mu Gode Allahu Mairahama)
Su ma
waɗɗannan baitocin ɗauke suke da wa’azi kamar sauran
da suka gabace su. A ciki ana gargaɗin Musulmi su guji ƙarya da
annamimanci da munafucci da ci-da-ceto da shan giya da girman kai da ƙwace da fahari da halattar da haram, aikata waɗanna na kawo rashin samun tsira
idan an je Lahira.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.