Ticker

6/recent/ticker-posts

Tafa-Tafa

6.31 Tafa-Tafa

Wannan wasa ne na yara mata. Yara biyu maza su iya gudanar da wasan a tsakaninsu. Sai dai wani lokaci akan yi shi tsakanin yaran da suka kai shida, ko ma sama da haka.

6.31.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko wurin jaura ko wani wuri da yara ke haɗuwa.

ii. Idan a dandali ake wannan wasa, yakan kasance da dare ne. Amma wani lokaci akan yi shi da hantsi ko da yamma, musamman a wurin jaura da ke tara hara da dama. A irin wannan lokaci, waɗanda suka sayar da kayan jaura za su iya wasanni daban-daban musamman yayin da suke jiran abokan tafiyarsu su ƙarasa sayarwa.

6.31.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya su fuskanci juna. Daga nan za su fara tafa hannuwansu cikin salo daban-daban. Sukan tafa hannuwan dama, sannan su yi tafi (kowa ta tafa da kanta, wato ta haɗa hannuwanta na dama da na hagu). Sai kuma su tafa da hannuwan hagu, su kuma sake yin tafi. Sukan yi haka cikin ƙwarewa da gwaninta kuma cikin gaggawa. Yayin da suke wannan wasa, sukan yi waƙa kamar haka:

Tafa-tafa,

Tafiyar nan da za mu gobe,

Da wa za mu yin ta?

Daga Allah sai Ma’aiki,

Sai ɗan yaro masoyi,

Ya masoyi jira ni,

In daka in kirɓa,

Kada kura ta ci mu tare,

Idan ta ci mu tare,

Allah ne gwanin iyawa,

Annabi ne gwanin iyawa,

Ke kaza da tone-tone,

Kada ki tono wa kanmu,

Abin duniya da rana tsaka fafal,

Ɗan mai dogon wuya zalam,

Haƙoransa da gari buɗu.

Yayin da aka saɓa wurin tafa hannu, to an ɓata a wasa ke nan. Saboda haka za a sako wasan daga fari. An samu wata waƙar ta daban da ake amfani da ita yayin wasan a ƙasar Katsina. Ta kasance kamar haka:

Muna tafa-tafa,

Akwai wanda nake so,

Amma kunya na so,

Ta wanke ni da soso,

In faɗa ku ji kar ku yi dariya,

Fari ne siriri,

Yana da tsawo ga gashi,

Ya iya kwalliya kamar ɗan sarki,

Na mori saurayi mai kyawu,

Allah Ya sa yana da halin kirki

Mu tafi mu ji daɗin zama,

Mu yi wasa mu yi dariya.

6.31.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Waƙar wasan na ɗauke da saƙon da ke nuni da cewa, duk abin da ya samu mutum to daga Allah ne. Wato dai tana koyar da imani da kuma tauhidi. Waƙar ta biyu kuwa, tana bayyana ƙudurin zuciya ta yaran da ke wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments