Ticker

6/recent/ticker-posts

6.3 Jigogin Waƙoƙin Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa6.3 Jigogin Waƙoƙin Bara

Bayan sanin ma’anar jigo sai kuma aka dubi jigogin da ake samu a cikin waƙoƙin bara. Duk da yake babban jigon waƙoƙin bara shi ne bara, wato roƙon jama’a taimako game da samun wani biyan bukata kamar na abinci ko sutura ko ma wani abin gudanar da rayuwa, amma kuma akwai wasu kalamai masu ɗauke da wasu saƙonni da suke amfani da su masu taimakawa ga saurin samun biyan bukata da mabarata ke ƙunsawa a cikin waƙoƙin nasu. Irin waɗannan saƙonnin ko jigogin sun haɗa da wa’azi irin zuhudu da madahu da ilmantarwa da na nishaɗantarwa da barkwanci da bantausayi da fatan alheri. Bayani kan haka tare da misalai zai zo daki-daki.


Post a Comment

0 Comments