Ticker

6/recent/ticker-posts

O Aliyo

6.30 O Aliyo

Wannan ma wasan gaɗa ne da ‘yanmata ke gudanarwa a dandali. Mutane da dama ne ke haɗuwa domin gudanar da wannan wasan. Yawansu kan kai ishirin ko ma sama da haka.

6.30.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen biki da aka samu taron yara mata.

ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

6.30.2 Kayan Aiki

Kallabi /Ɗankwali

6.30.3 Yadda Ake Wasa

Masu wasa sukan yi da’ira. Mutane biyu za su shiga tsakiya. Wasan yana tafiya da waƙa tare da tafi. Yayin da ake waƙar, waɗanda ke kan da’ira za su riƙa zagawa tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka: 

Bayarwa: O Aliyo,

O Aliyo,

O Aliyo.

Amshi: ’Yan mata.

Bayarwa: Ina mijinki ne?

Amshi: ‘Yan mata.

Aliyar Gwangola: Ya yi tafiya.

Amshi: ‘Yan mata.

Bayarwa: Tun watan nawa?

Amshi: ‘Yan mata.

Aliyar Gwangola: Tun watan bakwai.

Amshi: ‘Yanmata.

Bayarwa: Za ki bi shi ne?

Koko ba za ki bi shi ba?

Amshi: ‘Yanmata.

Aliyar Gwangola: Zan bi shi man.

Amshi: ‘Yanmata.

Bayarwa: Bi shi bi shi bi shi,

Bi shi mana,

Aliyar Gwangola.

Daga nan Aliyar Gwangola za ta fara tafiya a hankali, wato dai tana bin mijinta. Waƙa kuma za ta ci gaba:

Bayarwa: Haba dawo dawo dawo,

Dawo mana,

Amshi: Aliyar Gwangola.

A wannan gaɓa Aliyar Gwangola za ta riƙa dawowa da baya da baya.

Bayarwa: Haba mai da ɗankwali gindin goshi mana,

Amshi: Aliyar Gwangola

A wannan gaɓa Aliyar Gwangola za ta mayar da ɗankwalinta gaban goshi.

Bayarwa: Haɓa ɗebo shoki ki ba su kunya,

Amshi: Hasana a leda.

A wannan gaɓa dukkanin ‘yan wasa za su tsuguna ƙasa su yi wata ‘yar rawa da ake yi wa laƙabi da shoki. Waƙa kuma za ta ci gaba:

Bayarwa: Sosa abinki babu kunya,

Amshi: Hasana a leda.

Da an kawo wannan gaɓa to za ta fita, sai wata kuma ta shiga.

6.30.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana ɗauke da wani saƙo ga ma’aurata musamman ta hanyar nuna rashin dacewar miji ya bar matarsa na tsawon lokaci ba tare da ya waiwaice ta ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments