Ticker

6/recent/ticker-posts

Nayaya?

6.29 Nayaya?

Wannan ma wasan yara mata ne. Kimanin yara shida zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yana cikin jerin wasannin mata da ke tafiya da waƙa.

6.29.1 Wuri Da Lokacin Wasa

Kasancewar wasan na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

6.29.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Sai guda ɗaya kuma ta fito tsakiya. Daga nan za ta fara waƙa saura kuma na amsawa tare da tafi. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Ado Ado ne,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Ado Adona,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Ado mai tarago,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Idan ya kama aiki,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Ba ya so ya saki,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Sai an kai ga kadada,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Kadada ta biyu ce,

Amshi: Nayaya?

Bayarwa: Can nakuɗi na belbeji

Amshi: Nayaya?

Idan aka kawo wannan gaɓa, sai yarinyar ta koma cikin da’ira, wata kuma ta fito don ci gaba da wasa.

6.29.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. A cikin waƙar wasan, kowace yarinya na ƙoƙarin nuna cewa, saurayinta mai ƙwazo ne da kuma jajircewa a kan aikin da yake yi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments