Ticker

6/recent/ticker-posts

A Sha Ruwa

6.2 A Sha Ruwa

Wasan A Sha Ruwa,ytana ɗaya daga cikin wasannin tashe. Yara mata ‘yan kimanin shekaru takwas (8) zuwa sama ke wannan wasa. Babu buƙatar wata shiga ta musamman. Sannan ba a buƙatar wani kayan aiki kafin farawa. Yawanci yawan yaran kan kai biyar (5) zuwa sama.

6.2.1 Lokacin Da WurinWasa

i. Babu wani takamaiman lokaci na gudanar da wannan wasa. Akan yi shi da safe ko da yamma ko kuma da dare. Sai dai a cikin azumi kaɗai ake yin sa, kasancewar sa wasan tashe. Wasu lokuta, yara na iya rera waƙar wannan wasa a lokacin wasanninsu. Amma ba hakan ke nuna suna aiwatar da wasan ba, kasancewar tashe na zuwa ne a lokacin azumi kawai. Saboda haka, a iya cewa, yara kan tuna da wannan wasa a lokacin da ba na watan azumi ba, har ma su rera waƙarsa.

ii. Dangane da wurin wasa ma, babu wani takamaiman wurin tsayuwa domin a yi wasan. A maimakon haka, akan bi gida-gida ne inda ɗaya daga cikin yaran za ta riƙa waƙa, saura kuwa su riƙa amsawa.

6.2.2 Yadda Ake Gudanar Da A Sha Ruwa

Yara za su zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin jagora, mai ba da waƙa. Daga nan za su riƙa shiga gida-gida jagora na bayar da waƙa saura kuma na amsawa. Za su yi ta maimaita waƙar har sai an kawo sadaka an ba su, ko kuma an sallame su ta hanyar cewa: “Allah Ya ba da sa’a.”

6.2.3 Waƙar Wasa

Jagora: Goma na marmari,

Goma na tilas,

Goma na ɗokin salla.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: A sha ruwa,

A sha ruwa lafiya.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: Masu gidan nan,

Bacci kuke ko salla?

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: In bacci ne,

Ku tashi domin Allah.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: In salla ce,

Ku yi ta domin Allah.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: In salla ce,

Ku yi ta domin Ma’aikin Allah.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: Watan azumi ne ai ta ibadar Allah.

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

 

Jagora: Na yi mafarki,

Inna tana aljanna,

A kan kujerar ƙarfe,

Mashimfiɗar zinari,

Buzun Ma’aikin Allah,

‘Y/Amshi: A sha ruwa.

6.2.4 Tsokaci

Wannan wasan tashe yana tunasar da jama’a cewa, watan azumi lokacin ibada ne ba na bacci ba. Sannan yana nusantarwa zuwa ga aikata aiki domin Allah, wato ba domin riya ba. Daga ƙarshe kuma yana albishir da ƙwadaitarwa zuwa ga Rahamar Ubangiji wanda ya danganci gidan Aljanna da ni’imomin da ke ciki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments