Ticker

6/recent/ticker-posts

Rana Ta Fito Gabas

6.28 Rana Ta Fito Gabas

Wannan ma wasan gaɗa ne na dandali. Kimanin yara goma zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

6.28.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Asalin wasan na dandali ne, amma akan gudanar da shi a makarantu ko gidajen bikin da aka samu taron yara mata.

ii. An fi gudanar da wasan da dare, ko lokutan makaranta.

6.28.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su yi da’ira, yayin da ɗaya daga cikinsu za ta shiga tsakiya. Wadda ke tsakiyar za ta riƙa ba da waƙa, yayin da sauran kuma ke amsawa tare da tafi. Yayin da suka ƙare, sai yarinyar da ke tsakiya ta koma cikin da’ira. Wata kuma za ta fito domin ci gaba da wasa.

6.28.3 Waƙar Wasa

Mai Bayarwa: Rana ta fito gabas,

‘Yan Amshi: Ta faɗa a yamma.

Mai Bayarwa: Ga wani malami ya fito,

‘Yan Amshi: Da baƙar takarda.

Mai Bayarwa: Shi ma malamin ba shi kunya,

Yan Amshi: Ba shi tsoro.

Mai Bayarwa: Iya,

‘Yan Amshi: Iya ga rawa-rawa ga rawa.

Mai Bayarwa: Iya ga rawar,

‘Yan Amshi: Kurege.

Mai Bayarwa: Yaro ba zai iya ba,

‘Yan Amshi: Ni ma da ƙyar na koya.

Mai Bayarwa: Da gudu da tsalle-tsalle,

‘Yan Amshi: Da fuka-fukin agwagwa.

Daga nan za a haɗa baki da mai bayarwa da masu amshi kamar haka:

Gwana-gwana,

Gwana ta kaɗa zare,

Ta ce gwani zo ka saya,

Sule talatin da biyar,

In ba biyar ba ciniki.

Mai kare kama karenka na ji kukan kura,

A ina?

A can tashar Gwangola,

Inda mata ke haihuwa maza na yaye.

Sharɓale-sharɓale,

Mai rigar zinare,

Alhajin da bai je haji ba,

Ya kama jaka ya ɗira,

Ya kai ta kantin sukari,

Can sukari can sukari tsurut?

6.28.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da raha da annushuwa ga masu yi da kuma masu kallo. Yaya aka yi suka koyi rawar kurege ta hanyar amfani da fuka-fukin agwagwa?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments