Ticker

6/recent/ticker-posts

Kin Zama

6.27 Kin Zama

Wannan wasa yana da zubi da tsari irin na wasan laula. Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ake gudanarwa a cikin kowanne. Waƙar da yara ke yi a wasan kin zama shi ne:

Bayarwa: Kin zama yarinya,

Amshi: Kin zama.

Bayarwa: Kin zama ɗauko riga,

Amshi: Kin zama.

Bayarwa: Kin zama ɗauko riga,

Amshi: Kin zama.

Bayarwa: Kin zama ɗauko hula,

Amshi: Kin zama.

Bayarwa: Kin zama ban takalmi,

Amshi: Kin zama.

Bayarwa: Kin zama kawo buta,

Amshi: Kin zama.

6.27.1 Tsokaci

Bayan nishaɗi da wannan wasa ke bayarwa, yana ɗauke kuma da wani saƙo zuwa ga amarya, da ke nuna mata yanzu fa tana da nauyi a kanta. Wato da aiki babba a gabanta na hidimar gidan aure. Sai dai akan faɗi wannan saƙo ne cikin waƙar a sigar shaguɓe.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments