Ticker

6/recent/ticker-posts

Carman-Dudu

6.1 Carman-Dudu

Wasan carman-dudu na buƙatar mata a ƙalla huɗu ko sama da haka domin gudanarwa. Za su iya kasancewa daga huɗu har zuwa goma, ko ma sama da goma. Sukan kasance ‘yan mata masu kimanin shekaru goma zuwa sama.

6.1.1 Wuri da Lokacin Gudanar Da Wasa

i. Yan mata na gudanar da wannan wasa a dandali, ko kuma a filin ƙofar gida.

ii. An fi gudanar da wannan wasa da dare, lokacin da babu wani aikin gida.

6.1.2 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

‘Yanmata sukan yi da’ira. Ɗaya daga ciki za ta fito tsakiyar da’irar ta riƙa yin waƙa, sauran kuwa za su riƙa amsa mata. A mafi yawan lokuta za su riƙa tafi tare da ‘yar rawa. Za su riƙa ‘yar duƙawa yayin ambaton amshi. A yayin da take waƙar, za ta riƙa bin abokan wasan ɗaya-bayan ɗaya tana dafa kafaɗarsu. Yayin da ta ƙare, wata daga cikin‘yan matan (mafiyawanci wadda aka dafa ta ƙarshe) za ta fito domin ita ma ta bayar da waƙar, sauran kuma su ci gaba da amshi. Haka za a ci gaba da yi, har sai kowacce daga cikinsu ta yi.

6.1.3 Waƙar Wasar Carman-dudu

Jagora: Carman-dudu carman-duduwa,

Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Akwai wani baƙo a gidan mai gari,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Ba ya bashi ba ya lamuni,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Ba ya neman‘yan matan gari,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Ko ya nema wa zai ba shi ne?

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Yaya talandiyo mana,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Ƙanwa talandiyo mana,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Carmandu mu ci kaza da ƙwai,

‘Y/Amshi: Carmande!

 

Jagora: Carman-dudu carman-duduwa,

‘Y/Amshi: Carmande! 

6.1.4 Tsokaci

Haƙiƙa waƙar wannan wasa tana isar da wani saƙo ga al’umma, cewa kada mutum ya kasance ramin kura daga ke sai ‘ya’yanki. Kamar yadda baƙon gidan mai gari ya kasance ba ya bashi ba ya lamuni, ma’ana ba ya hulɗa ko ta sisin kwabo da al’umma. Wannan ya sanya mutane ma suka watsa kashinsa. Har ta kai ga ko da ya nemi aure ba zai samu ba. Ke nan, dole ne mutum ya kasance mai kyakkyawar hulɗa da jama’a.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments