6.11 Hajiyar Ƙauye
Wannan ma wasan tashe ne. Yaran da ke gudanar da shi za su kai a ƙalla biyar zuwa sama da haka. Daga cikinsu akan cire shugaba wato mai waƙa. Sannan akan zaɓi Hajiyar Ƙauye. ‘Yan mata sukan bi gida-gida ne domin gudanar da wannan wasa. Sannan an fi yin sa da dare.
6.11.1 Kayan Aiki
i. Kayan shafe-shafe na kwalliyar mata kamar su janbaki da gazal da hoda da makamantansu.
6.11.2 Yadda Ake Wasar Hajiyar Ƙauye
Akan yi wa Hajiyar Ƙauye kwalliya da kayan shafe-shafe. Sannan takan sanya kaya masu ɗan kyau. Duk gidan da suka shiga domin wannan tashe, Hajiyar Ƙauye za ta kasance a gaba. Jagora kuma za ta riƙa ba da waƙa, sauran yara na amsawa. A wannan lokaci Hajiyar Ƙauye za ta riƙa‘yar rawa da rangwaɗa, wai ita a dole ta yi kwalliya ranar salla.
611.3 Waƙar Wasar Hajiyar Ƙauye
Jagora: Hajiyar ƙauye.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ta yi kwalliya ran salla.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ta yi ado ran salla.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ta yi arziki za ta gida.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ta sha hoda ta yi raɗau,
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ta yi kwalliya ran salla.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ga janbaki ya yi raɗau.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
Jagora: Ga kwallinta ya yi raɗau.
‘Y/Amshi: Hajiyar ƙauye!
6.11.4 Tsokaci
Wannan wasa yana nuni ga al’adar Bahaushe ta kwalliya ranar salla. Sannan yana kundace sunayen abubuwan kwalliyar mata. Ga ‘yan kallo kuwa, wasan yana samar da nishaɗi da annashuwa.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.