Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasar Gora-Gora

6.10 Wasar Gora-Gora

Wannan ma wasan ‘yanmata ne. Bai zama tilas a samu mutane da yawa ba domin gudanar da shi. Yara biyu ma kacal za su iya. Sai dai idan suka fi hakan abin ya fi armashi. Akan yi wasan da dare. Sai dai a ɗaiɗaikun lokuta  ba za a rasa ba da ake yi da hantsi ko da yamma. Ba a buƙatar wasu kayan aiki na musamman domin gudanar da wannan wasa. Sannan akan yi wasan a filin ƙofar gida, har ma a cikin gida wasu lokutan.

6.10.1 Yadda Ake Wasar Gora-gora

‘Yanmatan kan yi layuka biyu, suna fuskantar juna. Wato kowacce da wata a gabanta suna kallon juna. Daga nan za a samu jagora mai yin waƙa (idan sun wuce biyu). Idan su biyu ne kuwa, ɗaya daga cikinsu sai ta riƙa yin waƙar. Yayin da ta gaji, sai ɗayar ta karɓa. Za su riƙa tafa hannaye tare da ɗora ɗaya hannun a ƙirji. Ma’ana, yayin da suka tafa da hannun dama, to za su ɗora na hagu a ƙirji. Idan kuwa da hannun hagu suka tafa, sai su ɗora na dama a ƙirji. Za su ci gaba da haka cikin sauri da ƙwarowa, ba tare da kuskure ba. Wannan ya sanya ‘yan wasa dole su natsu tare da mayar da hankali, gudun yin kuskure.

6.10.2 Waƙar Wasa

Gora-gora,

Goran Iya da Baba,

Sun taru suna zagina,

Suka ce ba zan rama ba.

 

Na zagaya ban ɗaki,

Na tad da matar sarki,

Ɗaya da ciki ɗaya,

Da goyon ɗan zakara.

 

Ke wannan wa ya yi maki ciki?

In ba ki magani ya zube,

Zube ɗan farkan nan!

Zube ɗan farkan nan!

6.10.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki. Sannan za a iya hasashen ɓirɓishin zancen cikin shege da zubarwa daga waƙar wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments