Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Ciki

6.12 Mai Ciki

Wannan ma wasan tashe ne da ake gudanarwa cikin watan azumi. Yara shida zuwa sama da haka ke gudanar da wannan wasa. A cikinsu akan samu mai ciki (wadda za a yi wa cikin tsumma) da kuma shugabar wasa, wato mai ba da waƙa. An fi yin wannan tashe da dare, bayan an sha ruwa. Sukan bi gida-gida domin gudanar da wasan.

6.12.1 Kayan Aiki

i. Tsummokara

6.12.2 Yadda Ake Wasar Mai Ciki

Za a sanya wa Mai Ciki tsummokara a cikin riga, ya yi girma tamkar mai ciki. Sannan a ɗaure sosai yadda ba zai kwance ba yayin wasa. Yayin da suka shiga cikin gida, za ta kasance a gaba. Za ta riƙa tafiya da ƙyar irin ta masu ciki, tare da ɗora hannu a baya (dafe baya da babban ƙarewa). Daga nan jagora za ta fara waƙa saura suna amsawa. Mai Ciki kuwa tana ta fama da ciki.

6.12.3 Waƙar Mai Ciki

Jagora: Iye ga ni nan tafe.

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Iye ga ni nan tafe.

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Wallahi ba ni son sunan nan!

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Sunan uwar mijina ke nan.

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Wallahi za mu ɓata da mutum!

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Wallahi har gaban alƙali!

‘Y/Amshi: Mai ciki

 

Jagora: Wallahi ba ni son sunan nan!

‘Y/Amshi: Mai ciki

6.12.4 Tsokaci

Wannan wasa ya kasance tamkar madubin hango rayuwar mai ciki. Yana samar da nishaɗi ƙwarai ga masu kallo, musamman ganin yadda yara ke kwaikwayon mai ciki. Sannan yana nuna al’adar Bahaushe ta tsolayar mai ciki, duk da cewa cikin abin farin ciki da alfahari ne.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments