Ticker

6/recent/ticker-posts

Sillen Kara

6.102 Sillen Kara

Wannan ma wasan yara mata ne. Yana da zubi da tsari da kuma lokacin wasa irin na wasan Ni Karkashi. Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ake gudanarwa cikin wasannin. Waƙar wannan wasa ta sillen kara ta kasance kamar haka:

Bayarwa: Sillen kara

Amshi: Takanɗa.

 

Bayarwa: Aniyar kara,

Amshi: Takanɗa.

 

Bayarwa: In ba kara,

Amshi: Takanɗa.

 

Bayarwa: Me za mu sha?

Amshi: Takanɗa

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments