6.101 Ni Karkashi
Wannan wasa ne na yara mata da ke cikin rukunin wasannin dandanli. An fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Yara biyu ne suke gudanar da wannan wasa. Saboda haka, idan masu wasa suna da yawa, kowacce za ta haɗu da abokiyar wasa guda. Wasan na tafiya da waƙa, amma ba ta buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Yana kuma ɗaya daga cikin wasannin tsaye.
6.101.1 Yadda Ake Wasa
Yara za su juya wa juna baya. Sai kuma su sanya hannuwa cikin najuna. Wato kowacce za ta kasance rungume da hannuwan ‘yar’uwarta, amma ta baya. Sai kuma su fara goye-goye a haka nan. Wato É—aya za ta sunkuya ta janyo abokiyar wasanta yadda abokiyar wasan za ta kasance kwance kan bayan wadda ta janyo ta, kamar dai goyon kuwa. Sai kuma ta sauke ta. Ita kuma waccar ta yi haka nan. Za su riÆ™a waÆ™a yayin da suke wannan goye-goye kamar haka:
Bayarwa: Ni karkashi,
Amshi: Ni lalo.
Abayarwa: Mijina,
Amshi: Matata.
6.101.2 Tsokaci
Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Bayan haka, wasan na nuni ga dangantakar da ke tsakanin miji da mata, ta ƙut-da-ƙut.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.