Ticker

6/recent/ticker-posts

To Iya

6.100 To Iya

Wannan ma wasan tashe ne na yara mata. Sukan gudanar da shi da dare bayan an sha ruwa a watan azumi. Sannan sukan bi gida-gida ne domin gudanar da wasan. Yana kuma buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin yara biyar ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Daga cikinsu akwai mai fitowa a matsayin uwa, da kuma ake kiranta iya. Sai kuma sauran ‘yan wasa da suke kasancewa a matsayin ‘ya’yanta.

6.100.1 Kayan Aiki

i. Tabarma ko tabarmi

ii. Filo/matashin kai

iii. Kwanoni da wasu shirgi

iv. Zane ko kallabi babba da ake amfani da shi wurin ɗaure faggon kayan

6.100.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan nemi tabarma da filo/matashin kai da wasu tarkace kamar kwanoni da makamantansu. za su ka su nemi zane ko babban kallabi su ɗaure su wuri ɗaya. Daga nan yaran za su ɗunguma wurin tashe. Ɗaya daga cikinsu, wadda ta fi su girma a mafiyawan lokuta, za ta kasance uwarsu a cikin wasan. Sauran kuwa duka ‘ya’yanta ne. Saboda haka za su riƙa kiran ta da iya ita kuwa za ta kira su da ‘ya’yana.

Yayin da suka isa wurin da za su yi tashe, yara za su aje faggon da suka taho da shi. Sai kuma iya ta fara faman tattare-tattare tamkar dai wadda take faman haɗe kayanta wuri ɗaya domin tafiya wani wuri. Za ta riƙa yi tana waƙa. ‘ya’yan nata kuwa za su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take:

Iya: Ku zo ku zo ‘ya’yana,

Ya’ya: To iya.

 

Iya: Ubanku ya koro ni,

Ya’ya: To iya.

 

Iya: Saboda babbar loma,

Ya’ya: To iya.

Haka za su ci gaba da wannan waƙa. Yayin da ta kamala tarkata faggonta, za ta kinkime su. Sannan za ta ci gaba da kaɗa kan ‘ya’yan da nufin su tafi. Wato dai tamkar wadda mijinta ya kora da gaske.

6.100.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga masu gudanarwa da kuma musamman masu kallo. Sannan akwai ɓirɓishin nuna wani yanayi da aure kan shiga, a ƙasar Hausa. Wato ko dai yaji ko saki. An gina waƙar wasan bisa raha. Lallai riƙon Iya sai hukuma tun da manyan loma har na sa a kore ta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments