Ticker

6/recent/ticker-posts

Salamatu

6.9 Salamatu

Wannan wasa ne da ‘yanmata suke gudanarwa, musamman da dare lokacin farin wata. Akan yi shi a dandali ko filin ƙofar gida. Bayan samuwar makarantun boko, ‘yan makaranta suna yawaita wannan wasa a makarantu, lokacin tara. Babu wasu kayan aiki na musamman da ake buƙata domin gudanar da shi.

6.9.1 Yadda Ake Wasan Salamatu

‘Yanmatan sukan jeru wuri ɗaya, a manne da juna. Ɗaya daga cikinsu kuma za ta kasance a gaba. Wacce take gaban za ta riƙa ba da amsa, sauran suna amsawa tare da tafi. Yarinyar za ta riƙa faɗowa jikinsu. Su kuwa sai su riƙe ta yadda ba za ta kai ƙasa ba, su tallafo ta su miƙar da ita tsaye. Haka za ta ci gaba da faɗa musu a duk lokacin da ta kai ƙarshen ɗangon waƙarta. Su kuwa sukan miƙar da ita tsaye daidai lokacin da suke ambatar amshin waƙar (iye). Yayin da ta yi wa nata, sai ta dawo cikin‘yan matan. Wata kuma ta fita ta yi haka nan. Haka za su yi ta yi har kowace sai ta kasance jagora.

6.9.2 Waƙar Wasar Salamu

Jagora: Ba za ni ba za ni ba,

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ba za ni Kaduna ba.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Kaduna da mene ne?

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Kaduna Mayu ne!

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Sun ci mutum tara.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Na goma suke jira.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Allah mai ɗaukaka.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ya ɗauki Salamatu.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ya kai ta gidan sama.

‘Yan mata: Iye

 

Jagora: Ga madara ga zuma.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ga dambun alkama.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ga dambun nakiya.

‘Yanmata: Iye

 

Jagora: Ga madara ga maɗi.

‘Yanmata: Iye

6.9.2 Tsokaci

Wannan wasa yana ɗauke da raha da nishaɗi. Yaran na nuna sha’awarsu da fatan samun gidan aure irin na Salamatu. Akwai kuma ɓirɓishin barkwancin gari a cikin waƙar. Hakan na nuna cewa, idan aka samu irin wannan wasan a wani gari na daban, garin mayu zai tashi daga Kaduna ya koma wani daban (da ya kasance akwai barkwanci tsakaninsa da garin masu gudanar da wasa). Shin ba a taimako ga mayun Kaduna da bawa ko guda ne daga Kano su mai da kwaɗayinsu?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments