Ticker

6/recent/ticker-posts

5.7.1 Ma’anar Hikimomin Jan Hankali (Falsafa)

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.7.1 Ma’anar Hikimomin Jan Hankali (Falsafa)

Su ne hikimomin Falsafa, falsafa kalma ce da ta samo asali daga harshen Girkanci. Kalmomi biyu suka haɗu suka tashe ta, wato kalmar “Philo” mai nufin ƙauna da ta “Sophia” mai nufin hikima. Ma’ana tana nufin ƙauna da hikima na ƙoƙarin zurfafa tunani tare da nazarin abin da yake kai-komo a sararin subuhana, tare da hikimar bayaninsa (Encyclopedia of religion and Ethics 1953).

A ƙamusun Al-Maurid an bayyana ma’anar kalmar falsafa da cewa:

Ilimi ne da ke tsara ilmummukan magana da ɗabi’u da siffar kyau da tunani na hankali ko wani tsari na addini ko wani fage na nishaɗi na mutum, ko kuma aƙida da fahimtar matsayi na wani mutum ko wasu jama’a”Al-maurid (1977).

Wannan ma’anar ta yi daidai da wadda ta gabace ta, mai maganar hikima da zurfaffa tunani ga yadda rayuwar yau da kullum ke gudana tare da bayar da ma’ana ga kowane abu ta hanyar tunani da hikima. Wanna ƙila shi ya sa Aminu (2004) ya ce:

“Bakin masana ya haɗu a kan falsafa hanya ce ta tunani da ƙoƙarin samun bayanan dukkan al’amurran da suka shafi duniya da ɗan Adam da inda ya sa gaba” Amin (2004:28).

Abinda malamin ya faɗa ƙarfafawa ne ga bayanan da suka gabata masu ƙoƙarin bayyana ma’anar kalmar falsafa. A bisa haka ake iya cewa kalmar falsafa na nufin yin tunani mai zurfi ta hanyar hikima domin samar da hasashe mai ma’ana domin fahimatar al’amurran duniya kamar aƙida ko wani abu. To idan kuwa wannan shi ne ma’anar falsafa, to akwai irin waɗannan hikimomin da ke ƙunshe cikin waƙoƙin bara da ga alama masu bara suke son jama’a su hango su kuma su lura da su.


Post a Comment

0 Comments