Ticker

6/recent/ticker-posts

Guro ko 'Yar Guro

 5.7 Guro/’yar Guro

Wannan ɗaya ne daga cikin wasannin Hausawa dangin dara. Mutane biyu ne ko sama da haka suke gudanar da shi. Yana ɗaya daga cikin wasannin da ake ɗora caca a kansu. Yara ne suka fi gudanar da wasan, amma manya kan yi wani lokaci, musamman ‘yan caca.

5.7.1 Lokaci Da Wurin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa da safe da kuma yamma, wani lokaci har da dare.

ii. Da yake wasan zaune ne, akan iya gudanar da shi a kowane wuri. Sai dai an fi yin sa a ƙarƙashin bishiya mai inuwa, ko kuma ma wani ɓangare daga cikin kasuwa, musamman ga ‘yan caca. Sannan an fi gudanar da wasan a lokacin damina, yayin da ƙasa ta kasance tana da damshi.

5.7.2 Kayan Aiki

i. Ƙananan duwatsu ko ‘ya’yan bishiyar kanya ko wani abu makamancin wannan.

 

5.7.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Za a yi ‘yan gurabu guda goma ko goma sha biyu ko goma sha huɗu waɗanda ake kira gida. Za su kasance a layuka guda biyu, misali biyar a layin farko, biyar kuma a layi na biyu. Daga nan za a sanya ‘ya’yan wasa uku-uku a kowanne gida (akwai lokutan da ake amfani da ‘ya’ya huɗu-huɗu a maimakon uku-uku). Daga nan za a raba gidaje. Idan mutane biyu ne ke wasan, kowa zai ɗauki layi ɗai-ɗai, wato gidaje biyar-biyar idan wasan mai gida goma ne. Idan sun kai uku ko huɗu ko sama da haka, za su raba gidajen daidai da daidai a tsakaninsu. Wasu lokuta yakan zama tilas wani ya samu gidaje da suka haura na saura ko suka yi gaza na saura. Yayin da mutum ya samu gidajen da suka gaza na kowa, to shi ne yake fara tafiya. Idan kuwa ya samu gidajen da suka fi na kowa yawa, to shi ne na ƙarshen tafiya, kuma na ƙarshen ɗaukar guro.

 

Da zarar an gama raba gidaje, sai kuma a fara wasa. Mai tafiya zai ɗebi ‘ya’yan gida guda sannan ya fara bin gidajen ɗaya bayan ɗaya yana ajiye ɗa ɗai-ɗai a duk gidan da ya iske. A gidan da ya ajiye ɗan ƙarshe, sai ya ɗebe ‘ya’yan wannan gida ya ji gaba da tafiya da su. Yayin da kuma ya ajiye ɗan ƙarshe na hannunsa a gidan da babu ɗa ko ɗaya, to ya yi kanda ke nan, tafiyarsa ta ƙare haka nan. Sai mai bi masa kuma ya karɓa. Wannan ya danganta da ko dai tafiyar tana yin hagu ne ko kuma dama.

 

Yayin da ake cikin tafiya, duk gidan da ya kasance da ‘ya’ya biyu, to an samu ciki ke nan. Da zarar sun zama uku kuma, an haihu. Yayin da aka haihu kuwa, mai gidan zai ɗebe haihuwar. Idan kuma ya bari har aka ƙara ɗora wani ɗa a kan haihuwar, shi ke nan ta ƙone. Saboda haka ya yi hasarar ta. Lokacin da kuma ya kasance mai tafiya ya ajiya ɗan ƙarshe na hannunsa a kan ciki ne, to zai ɗauke shi ko da a gidansa yake ko kuma ba a gidansa ba. Idan haka ta faru, ya shanye cikin ke nan. Yayin da ake cikin tafiya, sai aka samu wani gida ya tara ‘ya’ya sosai kasancewar ba a taɓa tafiya da shi ba, masu wasa za su yi murna, saboda da zarar an fasa shi, za su sha lagwada. Akan kira irin wannan gida da guro. Yayin da tafiya ta kai ƙarshe, ‘ya’ya suka zama saura uku kacal a cikin gidaje, to za a bai wa wanda ya yi tafiya a matsayin guro.

 

Daga nan za a sake zubi. Yayin da mai wasan guro ya ga ya jawo gida ko gidaje, zai kasance mai farin ciki. Idan kuwa an janye shi, to zai kasance cikin baƙin ciki da jin haushi. Mafi akasari za a riƙa zolayar waɗanda aka ja, musamman idan an kai mutum bukka, idan wasan ba ‘yar bukka kora ba ne. Idan bukka kora ne kuwa, daidai ya ke da an tatike shi. Waɗanda aka tatike ma sukan sha zolaya.

 

Haka ɗai za a yi ta wannan wasa har sai mutum ɗaya ya janye dukkanin gidajen. Daga nan kuma za a sake sabon zubi ko kuma a waste idan yara sun gaji.

 

5.7.4 Sakamakon Wasa

Wanda aka mayar bukka ko aka tatike a guro yakan sha zolaya. Wani lokaci har yaro kan ɓata ransa.

 

5.7.5 Dokokin Wasa

Wasu daga cikin dokokin wasan guro su ne:

i. Wanda ya yi tafiya shi ke ɗaukar guro.

ii. Mai wasa ba shi da damar ya yi ta hagu a wasan da dama take yi.

iii. Yayin da Haihuwa ta ƙone, babu dammar mai gidan ya ɗebe ‘ya’yan.

iv. Yayin da aka tatike mai wasa, to an kore shi.

 

5.7.6 Tsokaci

Wannan wasa yana wasa ƙwaƙwalwa da sanya zurfin tunani ga yara. Domin kuwa dole ne yaro ya kasance mai zurfafa tunani da yin lissafi kafin ya kai labari a wasan guro. Idan ba haka ba, tashi ɗaya za a tatike shi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments