Ticker

6/recent/ticker-posts

Sabis

 5.6 Sabis

Za a iya hasashen cewa, wannan wasa ya samu ne bayan cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Turawa. Domin sunan wasan kansa ararriyar kalma ce daga Ingilishi (service). Haka ma zubin wasan na kama da kwaikwayon wasan ƙwallon gora. Mutane huɗu zuwa sama ne suke gudanar da wasan sabis.

 

5.6.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. An fi gudanar da wasan sabis a dandali ko wani keɓaɓɓen fili.

ii. Akan gudanar da wasan sabis da hantsi ko da yamma.

 

5.6.2 Kayan Aiki

i. Sandan sabis

ii. Sabis

 

5.6.3 Yadda Ake Gudanar Da Wasa

Akan nemo sanda mai laujen kai, a gyara ta. Daga nan kuma za a samu tsohon takalmi silifa. Za a yi amfani da wani abu mai kaifi a gyara shi zuwa rawul. Wani lokaci akan sanya kan tsohon tocila na ƙarfe a wuta. Idan ya yi zafi sai a ciro a ɗora bisa tsohon takalmin silifa a danna. Daga nan zai yanka rawul na takalmin mai kyau. Wani lokaci akan haɗa irin wannan rawul ɗin guda biyu ko uku a ɗinke da zare ko lilo domin ya yi kauri da nauyi.

 

Bayan Kayan Aiki  sun haɗu, za a raba wasa zuwa gari biyu. Akan yi rabiyar ta hanyar kira ko a samu mutum ɗaya ya raba. Yawanci kowane ɗan wasa yana son a haɗa shi da waɗanda suka iya waju. Bayan an raba ‘yan wasa zuwa gida biyu, sai kuma a shata layi da ke nuna tsakanin gidajen biyu.

 

Daga nan kuma za a fara ba da sabis, ta hanyar gara wa abokan wasa ƙwallon sabis. Kafin a yi haka, sai an tambayi idan sun shirya ta hanyar furta: “sabis!” Idan sun shirya za su ce: “Yes!” Idan kuwa ba su shirya ba za su ce: “Noo!” ‘yan wasa na yin amfani da sandunan hannunsu domin buga ƙwallon sabis zuwa gidan abokan karawa. ‘yan wasa suna da dammar amfani da sauran sassan jiki domin buga sabis ɗin. Misali ɗan wasa zai iya renon sabis zuwa jikin layi domin ya yi waju. Sannan zai iya sanya hannu domin raya sabis ɗin da ta suma. Duk lokacin da abokan wasa suka bugo sabis, ‘yan cikin gidan da aka bugo wa za su yi ƙoƙarin mayar da ita wancan gida. Duk wadda sabis ta mutu a gidansu, sun faɗi ke nan. Saboda da haka, abokan wasansu sun samu maki guda.

 

5.6.4 Dokokin Sabis

Dokokin sabis sun bambanta daga wuri zuwa wuri. Ga wasu daga cikin irin waɗannan dokoki:

i. Dole ne a sanar da abokan takara kafin a yi musu sabis.

ii. Gidan da aka yi wa sabis na da dammar ƙin saya yayin da aka yi mummunar sabis.

iii. Duk wanda ya yi sata zai fuskanci hukuncin ajiye sanda.

iv. Yayin da sabis ta mutu a kan layi, to za a yi faɗan layi.

 

5.6.5 Hukuncin Wasa

Wannan wasa yana tafe da hukunci ga wanda ya yi sata. Hukuncin ko shi ne ajiye sanda. Wato ɗan wasa ya aje sandarsa a gidan abokan karawar su sannan ya fita waje na wani ƙayyadadden lokaci.

 

5.6.6 Tsokaci

Wannan wasa ya kasance hanyar motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da su bin doka kamar yadda karya dokar wasan kan sa a hukunta mutum.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments