Ticker

6/recent/ticker-posts

Jini Da Jini

5.9 Jini Da Jini

Wannan wasa ne na gargajiya. Misalin yara takwas ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Yana da sigar shugabanci na liman da ladan da kuma mamu.

 

5.9.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Jini da jini wasan maza ne na dandali.

ii. An fi gudanar da wannan wasa ne da dare, musamman bayan an ci abincin dare.

5.9.2 Kayan Aiki

i. Rigar da aka nannaɗe wadda ake amfani da ita wajen dukan wanda ya ɓata.

ii. Bishiya ko katanga ko wani wuri da za a nuna a matsayin sha.

 

5.9.3 Yadda Ake Wasa

Liman yakan tsaya a gaba. Ladan kuma tare da mamu za su yi sahu-sahu a bayan liman. Dukkanin ‘yan wasa za su nannaɗe rigarsu, wadda da ita ne suke dukan duk wanda ya ɓata. Daga nan liman zai bayar da sanarwa kamar haka:

“Za a fara, za a fara!”

Ladan zai maimaita wannan sanarwa. Daga nan kuma liman zai fara ambatan sunayen abubuwa ɗaya bayan ɗaya. Da zarar ya ambaci sunan abu, mamu za su amsa da danja idan har abin yana da jini a jikinsa. Idan kuwa ba shi da jini, to za su amsa da babu. Yayin da wani yaro ya kuskure, to ya faɗi. Don haka za a rufa shi da duka da rigunan da aka nannaɗe a hannunsa. Ba za a bar shi ba har sai ya sha. Ladan ne yake da hurbin bayyana wanda ake duka ya sha ko bai sha ba. Da zarar ladan ya bayyana cewa an sha, to za a dena duka. Daga nan kuma wanda aka daka shi ne zai kasance liman a yayin ci gaba da wasa. Misali:

Liman: Jini da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Rago da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Akuya da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Kaza da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Zakara da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Mota da jini.

Mamu: Babu!

 

5.9.4 Sakamakon Wasa

Wanda ya ɓata a wasan jini da jini yakan sha duka, har sai ya je ya sha. Akan doke shi ne da rigar da aka nannaɗa.

 

5.9.5 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da harshe, musamman sanin sunayen abubuwa. Bayan haka, wannan wasa yana sanya nutsuwa ga yara, kamar yadda rashin nutsuwa kan kai ga yaro ya sha duka yayin da ya ɓata wasa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments