Ticker

6/recent/ticker-posts

Malam Ka Ci Kusa

5.65 Malam Ka Ci Kusa

Wannan wasa ne na yara maza da ke ɗaya daga cikin rukunen wasannin tashe. Yana da zubi da tsari irin na wasan Ka Yi Rawa. Abin da ya bambanta su kawai shi ne; a wasan Malam Ka Ci Kusa, yara na tuhumar Malam ne kan cewa ya ci ɓera. Wato saɓanin wasan ka yi rawa inda yara ke tuhumar Malam da cewa ya yi rawa. Ga yadda waƙar wasan take:

Yara: Malam ka ci kusa,

Malam: ‘Yar katarar da nic ci?

Ku ce mini na ci kusa?

 

Yara: Malam ka ci kusa,

Malam: ‘yar hantar da nic ci,

Ku ce mini na ci kusa?

 

Yara: Malam ka ci kusa,

Malam: Don ɗan kan da nic ci,

Ku ce mini na ci kusa?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments