5.64 Na Ci Na Kasa Tashi
Wannan ma wasa ne na yara maza da ke cikin rukunin wasannin tashe. Yayin gudanar da wannan wasa, akan bukaci kayan aiki, wato tsummokara. Kimanin yara biyar zuwa sama da haka ne ke gudanar da wasan. Sannan yana tafiya da waƙa. Kamar sauran wasannin tashen Bahaushe, an fi gudanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.
5.64.1 Yadda Ake Wasa
Za a cusa wa ɗaya daga cikin masu wasa tsummokara a cikin riga. Daga nan sai ya yi zanzoro da rigar, wato ya cusa ƙasanta cikin wando. Cikinsa zai yi tulu kamar wata mace mai ciki. Wannan shi ake kira Baba. Sai kuma ya shige gaba, sauran yara na biye.
Yayin da aka je wurin wasa, Baba zai kwanta rigingine (cikinsa na kallon sama) ko kuma ya zauna ya miƙe ƙafafu sannan ya dafa hannuwansa ta baya. Zai ta mutsu-mutsu tamkar wanda yake ƙoƙarin tashi amma ya kasa. Zai kuma riƙa yin waƙa, sauran yara na amsawa. Ga yadda waƙar take:
Baba: Na ci na kasa tashi,
Amshi: Baba zari gare ka.
Baba: Ai tuwon ne da daɗi,
Amshi: Baba da sai ka daure.
Baba: Ai miyar ce da daɗi,
Amshi: Baba da sai ka daure.
Baba: Ai tuwon har da nama,
Amshi: Baba da sai ka bar shi.
Baba: Ni ko na tsame naman,
Amshi: Ga shi ka kasa tashi.
Baba: Ai ko na suɗe kwanon,
Amshi: Ga shi ka kasa tashi.
Baba: Ai ko na shanye romon,
Amshi: Ga shi ka kasa tashi.
5.64.2 Tsokaci
Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan wasan na hannunka-mai-sanda ne game da cin abinci fiye da ƙima. Wato kamar dai yadda sakamakon ci fiye da ƙima ya jefa Baba cikin wani hali. An gina wasan ne kan raha da ban dariya. Domin duk wanda ya ga cikin Baba…
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.