Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka Yi Rawa

5.63 Ka Yi Rawa

Wannan ma wasan yara maza ne da ke cikin rukunin wasannin tashe. Kayan aikin da ake buƙata sun ƙunshi kayan maza tsofi da kuma auduga domin yin gemu sai sandan dogarawa yayin tafiya. Kimanin yara biyar ne suke gudanar da wannan wasa. Sannan wasan na tafiya da waƙa. Kamar sauran wasannin tashe, an fi gudanar da su da dare, bayan an sha ruwa.

5.63.1 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin masu wasa zai yi shigar maza tsofi. Zai sanya babbar riga da rawani da hula sannan a yi masa gemu da saje na auduga. Sai kuma ya riƙe sanda domin dogarawa domin tafiya. Wannan shi ake kira Malam. Haka za a ga yana tafiya a sussunkuye, tamkar dai tsoho ne na haƙiƙa.

Malam zai shige gaba, sauran yara masu wasa na biye. Yayin da aka iso wurin wasa, yara za su riƙa sa waƙa, shi kuwa Malam yana amsawa. Ga yadda abin ke kasancewa:

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da gemuna?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da carbina?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da rawanina?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Da allona?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: A ina wai?

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ƙarya ne.

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ban yi ba.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: Ku ji sharri.

 

Yara: Ka yi rawa kai Malam ka yi rawa,

Malam: To bari in taɓa

Da zarar malam ya ce bari ya taɓa, sai kuwa ya hau tiƙar rawa. Zai yi ta taƙarƙarewa yana rawa a sunkuye, tamkar dai tsoho ne ke wannan rawa.

5.63.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga masu kallo. Sannan wasan na ɗauke da hoton ɗaya daga cikin mutanen da ke cikin rukuni mai daraja ga al’adar Bahaushe; wato malami. Wanda daraja da girmansa sukan sa a yi masa tsammanin halayen nitsuwa da dacewa. Za a fahimci hakan yayin da Malam ke ba da hujjojin cewa bai yi rawa ba. Ya nuna ai yana da gemu ga carbi, ga rawani ga allo da dai makamantansu. Baya ga haka, wasan yana nuna wata ɗabi’ar malamai ta ƙoƙarin kare kai da kafa hojjoji a kan wani batu da ake taƙaddama kansa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments