5.62 Robali/Kyauro ‘Yar Sharel
Wannan ma nau’in wasan yara maza ne da ake gudanarwa da robali. Sai dai ta bambanta da wasannin robali na jifa da kuma taru. Su dai waɗancan sun ƙunshi jifa ko harbi. ‘yar sharel kuwa wasan zaune ne. Amma game da wuri da lokacin wasa, daidai yake da sauran wasannin robali da aka ambata a sama, ƙarƙashin 5.62 da 5.61.
Masu wasan ‘yar sharel sukan zana ƙaramar da’ira a ƙasa. Daga nan za a karɓi robali a hannun kowa, adadin da aka ƙayyade. Zai iya kasancewa ɗaya-ɗaya, ko biyu-biyu ko ma sama da haka. Za a sanya waɗannan robali da aka karɓa a tsakiyar da’irar da aka zana. Akan ajiye su ne a haɗe ba a watse ba.
Bayan komai ya kammala, kowane yaro zai cire takalminsa silifa. Wanda ba shi da shi, zai nemi aro a hannun wani yaron daban. Da wannan takalimi ne za a riƙa bugun tarin robali da aka ajiye cikin da’irar. Za a riƙa yin hakan ne ɗaya bayan ɗaya. Wato da wannan ya buga, sai na gefensa ya yi.
Burin kowa shi ne yayin da ya buga, a samu robali da suka rabu da sauran. Wato suka kasance sun sauka daga kan sauran robali, sun kasance kwance a ƙasa kawai. Idan haka ta faru, to zai ɗauke wannanro bali da ta rabu da ‘yan’uwanta; ya cinye ta ke nan. Wani lokaci yaro na sa’ar cin robali biyu ko ma sama da haka a lokaci guda. Haka za a ci gaba da yi har sai an cinye dukkanin robali da ke cikin da’irar.
5.62.1 Wasu Dokokin Wasa
i. Idan wata ko wasu robali suka hau layin da’irar da aka zana, ko suka fita waje, to mai yi ya faɗi. Don haka za a ƙara tattara su, a haɗe su wuri guda.
ii. Akan yi bugu da bayan takalmi ne kawai, ba a so a ja ko a tura yayin da aka yi bugun. Akan kira ha ko turawa yayin da aka buga sharel. Wanda ya yi sharel kuwa ya faɗi. Don haka ko ya ci, za a mayar da wadda ya ci kan ‘yan’uwanta.
iii. Mai wasa na da damar ba da aro ko kyautar robali yayin da za a yi zubi.
5.62.2 Tsokaci
Wasanni uku na robali da aka yi bayaninsu ƙarƙashin 5.61 da 5.62 da kuma 5.63 sun kasance hanyar samar da nishaɗi ga yara. Sannan yara sukan koyi ƙwarewar saitin jefa da na duka sakamakon waɗannan wasanni. Domin kuwa ko bayan sa’a, sukan bukaci ƙwarewa da kuma dabara.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.