5.62 Robali/Kyauro ‘Yar Taru
Wannan ma wasan yara maza ne da ake amfani da robali yayin gudanar da shi. Dangane da wuri da lokacin wasa, ba shi da bambanci da wasan robali ‘yar jifa. Sai dai zubi da tsarinsu ya bambanta.
A wannan wasa, akan zana gidajen dara ne masu ɗan faɗi kaɗan a ƙasa. Sukan kasance huɗu ko shida ko takwas ko ma goma. Daga nan za a rubuta wa kowane gida lamba a cikinsa. Ga misali a ƙasa:
8 | 7 |
6 | 5 |
4 | 3 |
2 | 1 |
Ɗaya daga cikin masu wasa zai zauna a gefen wannan gidan dara. Akan kira shi da suna mai taru ko mai kanti. Sauran yara kuwa za su koma can baya, su ba da tazara daga wurin da aka yi zanen. Kamar yadda ake robali ‘yar jifa¸ a wannan wasa ma akan ja layi wanda duk wani mai wasa a kansa zai tsaya.
A wannan wasa ba a buƙatar tirke. Abin da kawai ake buƙata, shi ne mai wasa ya sanya robalinsa tsakiyar ɗaya daga cikin gidajen dara da aka zana aka kuma yi musu lambobi. Idan mai jifa ya jefa waje, ba cikin gidan dara ba, to mai kanti zai ɗauke ta ya ajiye a gefe guda. Haka ma idan kan layi mutum ya jefa. Robali da aka tara, (na waɗanda ba su jefa cikin gida a daidai ba), su ake kira kanti.
Duk ɗan wasa da ya jefa robali gidan ɗaya, to mai kanti zai dawo masa da abarsa. Idan kuwa gidan biyu ya jefa., mai kanti zai ƙara masa guda ɗaya daga cikin kanti, su zama biyu ke nan. Haka dai abin ke kasancewa. Yayin da mutum ya jefa a gidan takwas, mai kanti zai ƙara masa guda bakwai daga cikin kanti.
5.62.1 Wasu Dokokin Wasa
i. Za a ba wa mai jifa adadin robali daidai da lambar gidan da ya jefa robali zuwa ciki.
ii. Wanda ya jefa wajen gida ko kan layi, to ya faɗi.
iii. Yayin da aka yashe kanti, mai kanti zai iya karɓar aro daga hannun mai arziki. Mai arziki kuwa shi ne wanda ya tara robali da yawa a hannunsa. Idan kanti ya cika, to za a mayar wa wanda aka yi aro daga gare shi robalinsa.
iv. Idan aka yashe kanti kuma ba a samu aro ba, to za a ci gaba da bin kanti bashi. Duk lokacin da kanti ya cika, za a ba wa masu bin bashi abinsu.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.