Ticker

6/recent/ticker-posts

Baban Dudu

5.59 Baban Dudu

Wannan ma wasan yara ne da ke cikin rukunin wasannin tashe. Kimanin yara huɗu ne zuwa sama suke gudanar da shi. Sannan yana tafiya da waƙa. Baya ga haka, akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashen ƙasar Hausa, ana gudanar da shi ne da dare, bayan an sha ruwa.

5.59.2 Kayan Aiki

i. Kayan tsofi maza kamar su babbar riga da hula da rawani

ii. Auduga

iii. Tsohuwar jaka ko babbar leda

iv. Tsummokara

v. Sandan dogarawa

5.59.3 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin yara zai yi shigar tsofi ta hanyar amfani da kayan da aka ambata a ƙarƙashin 5.59.2 da ke sama. Sannan za a masa gemu da saje na auduga. Zai kuma riƙe sanda domin dogarawa yayin tafiya. Bayan haka kuma, zai rataya tsohuwar jaka ko leda da aka cika da tsommokara. Wannan yaro shi ake kira da Baban Dudu.

Yayin da aka iso wurin tashe, Baban Dudu zai riƙa tafiya da faggon kaya niƙi-niƙi. Sauran yara za su sa waƙa, shi kuwa yana amsawa. Ga yadda waƙar take:

Yara: Baban Dudu zai gudu.

Baban Dudu: Don Allah ku bar faɗa,

Auren Dudu ya matso,

Ban da kuɗin sayen gado. 

5.59.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana nuna wani hali ko yanayi da magidanta ke iya shiga yayin aurar da ‘ya’yansu. Wannan ne ma ya sanya Bahaushe ke da al’adar gudummuwa yayin da aure ya taso. Kamar dai yadda Bahaushen ke cewa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Sannan hanu da yawa, maganin ƙazamin tuwo. Sai dai duk da haka, halin da Baban Dudu ya yi ba na kirki ba ne, wannan ne ma ya sa ba ya so a ji cewa zai gudu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments