Ticker

6/recent/ticker-posts

Tashi Wali

5.60 Tashi Wali

Wannan ma wasan tashe ne na maza da ke cikin rukunin wasannin tashe. Kimanin yara huɗu zuwa sama da haka ake gudanar da shi. Sannan wasa ne da ke buƙatar kayan aiki. Kamar sauran wasannin tashe, an fi gudanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.

5.60.1 Kayan Aiki

i. Hula da rawani

ii. Alkyabba ko wata riga mai faɗaɗan hannaye

iii. Carbi

iv. Auduga

5.60.2 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin masu wasa zai sanya hula da rawani sannan a yi masa gemu da saje na auduga. Zai kuma sanya alkyabba ko wata riga mai manyan hannaye buru-buru. Sai kuma ya nemi dogon carbi ya riƙe a hannu. Wannan shi ake kira Wali.

Yayin da aka je wurin tashe, waliyi zai riƙa buɗa hannuwa yana faman yunƙurawa sama, kamar dai mai tashi. Zai kuma riƙa sanya waƙa, sauran yara suna amsawa. Ga yadda waƙar take:

Wali: Wali zai tashi,

Amshi: Kar ka tashi wali.

 

Wali: Zan tashi,

Amshi: Kar ka tashi Wali.

 

Wali: Zan lula,

Amshi: Kar ka tashi wali.

 

Wali: Zan cilla,

Amshi: Kar ka tashi Wali.

Haka dai za a ci gaba, har sai an sallame su.

5.60.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ƙwarai, musamman ga masu kallo. Sannan yana ɗauke da ɓirɓishin wani tunani na Bahaushe dangane da waliyi. Wato kan cewa sukan yi abubuwa ban mamaki da dama, daga ciki har da tashi sama. Sai dai an gina wasan ne kan raha da ban dariya. Da Aku Waziri ya san da wannan Wali, lallai da ya masa kashedi cewa, ko ‘yan Sama Jannati ba su wanye da daɗi ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments