Ticker

6/recent/ticker-posts

Garere/Gare/Gare-gare

5.58 Garere/Gare/Gare-gare

Wannan ma wasa ne na yara maza. Yana da zubi da tsari irin na wasan taya. Abin da ya bambanta su kawai shi ne, akan yi amfani ne da taya yayin da ake wasan taya.Wasan garere kuwa akan yi shi ne da garere. An fi amfani da gareren keke a matsayin mota.

Wani bambancin wasan taya da na garere kuma shi ne, a wasan taya akan kaɗa tayar ne da kaya ko itace ko wani abu mai kama da wannan. A wasan garere kuwa tura garen ake yi ba kaɗawa ba. Wannan ko na faruwa ne musamman da yake gareren na da wani kwarmi da ke ba da dammar yaro ya sa kara ko wani abin turawa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments