5.57 Taya
Wannan ma wasa ne na yara maza. Yana cikin rukunin wasannin da ba ya tafiya da waƙa. Sai dai akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Yaro guda ma zai iya gudanar da wannan wasa shi kaɗai. Amma a wasu lokutan yara kan taru wuri guda domin gudanar da shi.
5.57.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Babu wani takamaiman wuri da aka ware domin gudanar da wannan wasa.
ii. Yakan kasance a cikin gida ko ƙofar gida ko dandali.
iii. Wannan wasa akan yi shi ne lokacin da ido ke ganin ido. Wato akan yi shi kowane lokaci in ban da dare. Akan yi wasan musamman lokacin da aka aiki yaro wani wuri ko lokacin da ya fita da niyyar zuwa wurin abokansa.
5.57.2 Kayan Aiki
i. Taya abin hawa (an fi amfani da tayar mashin)
ii. Kara ko siririn itace ko wani abu makamancin wannan
iii. Igiya (ba kodayaushe ake amfani da ita ba)
5.57.3 Yadda Ake Wasa
Mai wasa zai samu tayar wani abin hawa, musamman na mashin/babur. Zai kuma nemi kara gajere ko siririn gajeren itace ko wani abu mai kama da wannan. Ga mai wasa, wannan taya kamar mota ce, kara ko itacen hannunsa kuma abin tuƙi. Hanyar tuƙa motar kuwa shi ne, a gara wannan taya sannan a ci gaba da kaɗa ta ko tura ta gaba da wannan kara ko itace.
Wani lokaci akan ɗaura igiya ko wani ƙyalle a jikin tayar, sannan a riƙe ƙarshen ƙyallen. Akan kira wannan da suna birki. A duk lokacin da yaro zai tsayar da tayarsa, zai ja wannan ƙyalle ne kawai.
A duk lokacin da aka aiki yaro zuwa wani wuri, zai ɗauki wannan taya tasa (wadda lokuta da dama yara ke kira mota) ya tafi da ita. Sau da dama iyaye ma kan so yaro ya je da mota, saboda kuwa zai fi sauri. Wannan na faruwa ne kasancewar yaron da ke tafiya da taya, ba a hankali yake tafiya ba. Yakan gara ta ne da gudu, wani lokaci har ya riƙa dirin mota da bakinsa (jiiiiinnnnn). Idan wani ya sha gabansa yayin da yake tafiya, za ka ji har oda yake masa domin ya kauce (fii-fii-fiiiitt). Wannan ya sa wani lokaci idan uwa za ta aiki ɗanta, kuma tana so ya yi sauri, za ta ce da shi:
“Ɗauki motarka maza, ka yi sauri ka je ka dawo.”
Wasu lokutan yaran unguwa sukan haɗu domin a yi tseren mota. A irin wannan yanayi, yara za su shiga layi guda – su jeru. Sannan za a ƙirga daga ɗaya zuwa uku. Sai kuma a ranta a nakare kowa na gara tayarsa cikin gudun ya da ƙanin wani. Wasu tayarsu kan faɗi a hanya. Wasu kuma wurin sharer kwana ake barinsu a baya.
5.57.4 Tsokaci
Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Kuma hanya ce ta motsa jiki gare su. Akan kwaikwayi wani abin hawa ne da yake a zahiri. A rashin uwa sai a yi uwar ɗaki. Domin kuwa yara ji suke yi tamkar motar gaske suka shiga ko mashin na gaske suka hau.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.