Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsoho Da Gemu

5.56 Tsoho Da Gemu 

Wannan ma wasa ne na yara maza. Yana ɗaya daga cikin wasannin tashe. Akan yi amfani da kayan aiki da suka danganci shiga irin ta tsofi maza. Wannan ya ƙunshi babbar riga da hula da rawani, sai kuma gemu da saje da ake yi da auduga. Wasan yana tafiya da waƙa. Sannan kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka ke gudanar da shi. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashe, ana yin sa ne da dare bayan an sha ruwa.

5.56.1 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin yara zai yi shigar tsofi kamar yadda aka bayyana a sama ƙarƙashin 5.56. sannan zai nemi sandan dogarawa ya riƙe. Sauran yara kuwa za su kasance biye da shi. Yayin da aka je wurin tashe. Wannan tsoho zai ci gaba da tafiya a sussunkuye, yana dogara ‘yar sandarsa. Ɗaya daga cikin yara kuma zai riƙa ba da waƙa, saura na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Tsoho da gemu,

Amshi: Ya tsufa.

 

Bayarwa: A ba shi na Allah,

Amshi: Ya tsufa.

 

Bayarwa: A ba shi na Annabi,

Amshi: Ya tsufa.

 

Bayarwa: A taimako tsoho,

Amshi: Ya tsufa.

Bayarwa: Ba shi da ƙarfi,

Amshi: Ya tsufa. 

5.56.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo, yayin da suka dubi yadda yaro ya zama tsoho ƙarfi da yaji. Sannan wasan na nuni ga wani hali mai kyau na Bahaushe, wato taimakon mai ƙaramin ƙarfi, da rashin wulaƙanci ga tsofaffi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments