Ticker

6/recent/ticker-posts

Dantsoho Mai Cin Bashi

5.55 Ɗantsoho Mai Cin Bashi

Wannan wasarntashe ne na yara maza. Kimanin yara biyar zuwa sama da haka ne suke gudar da wannan wasa. Sannan akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Kamar yadda mafi yawan wasannin tashe suke, an fi gudanar da wannan wasa da dare.

5.55.1 Kayan Aiki

i. Kayan sawa na dattawa kamar babbar riga da hula da rawani

ii. Matashin kai/filo

iii. Sanduna guda biyu

iv. Igiya ko zane

5.55.2 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin yara zai yi shigar dattijo. Wato zai sanya babbar riga da hula da rawani, sannan ya riƙe sandan dogarawa. Za kuma a goya wawannan yaro filo a bayansa ta cikin wannan babbar riga. Akan ɗaure filon tamau da igiya ko zane yadda ba zai kwance ba. Wannan shi ake kira Ɗantsoho a cikin wasan. Da yake kuma babbar rigar ta rufe shi, sannan yaron a sunkuye zai riƙa tafiya a matsayinsa na tsoho, ba dole ne a gane akwai filo goye bayansa ba. Wani kuma daban daga cikin yaran zai riƙe sanda a hannunsa.

Yayin da aka je wurin tashe, yara za su riƙa faɗi a tare:

“Kai ɗan tsoho mai cin bashi, biya mu kuɗin bashinmu na bara.”

Da zarar sun faɗi haka, wanda ke riƙe da sanda zai dubi bayan tsoho ya tima masa sanda. Sai dai ka ji ‘tim.’ Mai kallo sai ya ji ras a zuciya, ganin yadda ake bugun wannan Ɗantsoho. Ɗantsoho kuwa zai riƙa ihu yana cewa:

“Wayyo Allah za su kashe ni. Ku ba ni in ba su.”

5.55.3 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana shaguɓe ga mai wani hali, wato cin bashi. Mai cin bashi na banza da wofi dai kullum yana cikin wulaƙanci kamar yadda Ɗantsoho ya tsinci kansa a ciki. Sai dai an gina wasan kan raha da ban dariya. Domin ko ba komai, Ɗantsoho akwai taurin rai.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments