Ticker

6/recent/ticker-posts

Dan Bera

5.54 Ɗan Ɓera

Wannan wasan tashe ne na yara maza. Kimanin yara biyar zuwa sama da haka ne suke gudar da wannan wasa. Kayan aikin da ake buƙata yayin gudanar da shi sun haɗa da igiya da kuma bula ko baƙin tukunya. Wasan ba ya tafiya da waƙa, a maimakon haka, magana ce kawai ake yi tsakanin Ɗanɓera da sauran masu wasa. Kamar sauran mafiya yawan wasannin tashe, an fi gudanar da ita da dare.

5.54.1 Yadda Ake Wasa

Yara za su nemi igiya su ɗaura wa ɗaya daga cikinsu. Yawanci akan nemi ɗan ƙanƙani daga cikin masu wasa domin a ɗaura masa wannan igiya a ƙugu. Akan kira shi Ɗanɓera. Sannan za a shafe fuskar Ɗan Ɓera da bula ko baƙin bayan tukunya. Ɗaya daga cikin yara kuwa zai riƙe ƙarshen igiyar da aka ɗaura wa Ɗanɓera.

Yayin da suka je wurin wasa. Yara za su riƙa magana da Ɗanɓera, shi kuwa zai riƙa amsawa. Ga yadda abin yake:

Yara: Ɗanɓera mai shiga rami,

Ɗanɓera: Idan na shiga kar ku jawo ni.

Yayin da ake haka, Ɗanɓera zai riƙa ƙoƙarin cusuwa wani lungu ko saƙo da ke cikin gidan ko wurin da suke tashen (idan a dandali ne). wani lokaci har abubuwan da ke ajiye kamar tabarma ko likidiri/bokiti da makamantansu, zai riƙa ɗagawa domin ya shiga ƙarƙashinsu. Wanda ke riƙe da igiyar da aka ɗaure shi kuwa, zai riƙa janyo shi baya yana hana shi shiga wuraren da yake son shiga.

5.54.2 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Domin abin ya fi ga kwaikwayon halayyar ɗan Adam kawai, ya koma kwaikwayon halayyar dabba. An gina wasan kan raha da ban dariya. Domin ko ba komai za a ga babban ɓera mai magana.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments